An kori ’yan sanda 7 daga aiki kan yi wa jama’a kwace

Wasu ’yan sanda da ke yawo da na’urar cirar kuɗi ta POS suna kwatar kuɗaɗe daga hannun mutane sun rasa aikinsu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Imo, Mohammed Barde, ya ce jami’an da aka kora su bakwai sukan kama mutane su tafi da su a wata mota zuwa wasu wurare na musamman su kwace musu kuɗaɗe.

Ya ce, dubun jami’an da aka kora ta cika ne bayan rundunar ta samu ƙorafi daga jama’ar gari kan abin da suke aikatawa.

Ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis a Owerri, baban birnin jihar, cewa an gano jami’an sukan yi sintiri ɗauke da na’urar cirar kuɗi ta POS, wadda suke amfani da ita wajen karɓar kuɗi daga asusun bankin mutanen da suka kama.