Za mu buƙaci kowace ƙasa ta sanya sunan Pele a filin wasanta – FIFA

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta ce za ta buƙaci ƙasashen duniya kowacce ta sanya wa filin wasannin motsa jikinta sunan gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar nan da ya mutu kwannan nan, wato Pele.

FIFA za ta buƙaci hakan ne domin ci gaba da raya sunan marigayin wanda ya yi zarra a fagen wasan ƙwallon ƙafa a duniya.

Pele, wanda ɗan asalin ƙasar Brazilia ne, ya kwanta dama ne a makon da ya gabata inda ya bar duniya yana da shekara 82.

Da yake jawabi a wajen jana’izar marigayin a ranar Litinin, Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya ce “Za mu buƙaci duka ƙasashen duniya kowacce ta duba ta sanya wa ɗaya daga cikin filayen wasanta sunan Pele.”

Ya kara da cewa, dalilin hakan shi ne domin bai wa ‘yan baya masu tasowa damar sanin muhimmancin Pele a duniyar ƙwallon ƙafa.

Dandazon jama’a suka hallara birnin Vila Belmiro don shaida jana’izar marigayin wanda aka yi wa laƙabi da ‘Sarkin Ƙwallon Ƙafa na Duniya’.