Buhari ya rattaɓa hannu a kasafin 2023

Daga BASHIR ISAH

A ranar Talata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rattaɓa hannu a kasafin 2023 na Naira tiriliyan 21.83.

Rattaɓa hannun ya haɗa da na ƙarin kasafin 2022 da Majalisar Tarayya ta sahale wa Buharin.

Wannan dai shi ne karo na takwas kuma na ƙarshe da Buhari zai rattaɓa wa Kasafin Ƙasa hannu tun bayan da mulkin ƙasa ya koma hannunsa kusan shekara takwas da suka gabata.

Da yake jawabi, Buhari ya ce an samu ƙarin tiriliyan N1.32 kan tiriliyan N20.51 da aka kasafta tun farko wanda hakan ya sa kasafin ya ƙaru zuwa tiriliyan N21.83.

Shugaban ya ce ƙarin da aka nema kan kasafin 2022 zai taimaka wajen mangance matsalolin da suka faru a sakamakon mabaliyar ruwan da aka fuskanta a bara.

Ya ce kamar yadda aka saba, za a riƙa samun ƙarin haske lokaci-lokaci game da tafiyar da kasafin daga bakin Ministan Kuɗi, Kasafi da Tasare-tsare.

Ya ce yayin da wa’adin gwamnatinsa ke ƙaratowa, za su yi dukkan mai yiwu wajen aiwatar da muhimman tsare-tsaren da za su taimaka wajen bunƙasa walwalar ‘yan ƙasa da haɓaka harkokin kasuwanci da sauransu.