An kusan kammala aikin gina babbar gada a Abidjan

Daga CMG HAUSA

A ran 22 ga wata, wani kamfanin ƙasar Sin ya kammala aikin haɗa gefuna biyu na wata babbar gada da aka gina ta a Bangko Bay na Abidjan, cibiyar tattalin arzikin ƙasar Cote d’Ivoire.

Mashawarcin tattalin arziki da kasuwanci a ofishin jakadancin ƙasar Sin dake Cote d’Ivoire, Lu Jun ya halarci bikin murnar kammala aikin, har ma ya bayar da wani jawabi.

A cikin jawabi nasa, Lu Jun ya ce, an riga an sanya aikin a cikin shirin ci gaban ƙasar Cote d’Ivoire, ana fatan kamfanin Sin ya yi ƙoƙarin gaya tare da ɓangarorin Cote d’lvoire wajen kammala wannan muhimmin aiki, ta yadda za a iya ƙaddamar da shi da wurwuri.

A sa’i ɗaya kuma dole ne a tabbatar da inganci da tsaron aikin yadda ya kamata, a cewar Lu Jun.

Ya kuma ƙara da cewa, ana fatan za a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Sin da Cote d’lvoire, ta yadda zumuncin al’ummun ƙasashen biyu da dangantakarsu za su shiga wani sabon mataki.

An fara aikin gina babbar gada mai tsawon kilomita 7.5 a Abidjan a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2018, wadda ta haɗa da wasu titunan birni da wasu ƙananan gadoji bakwai.

Wannan aiki, wani muhimmin ɓangare ne na titunan birnin Abidjan, wanda zai kyautata yanayin zirga-zirgar birnin Abidjan da kuma ba da gudummawa wajen hada birnin da sauran yankunan Abidjan.

Mai fassara: Safiyah Ma