An naɗa macen farko magatakarda a Jami’ar Tarayya ta Gusau

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Majalisar gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Gusau, Jihar Zamfara, ta amince da naɗin Hajiya Nafisa Barau Suleiman, a matsayin babbar magatakardar Jami’ar ta uku.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin yaɗa labarai da sadarwa Dr. Linus Akor.

Dakta Linus Akor ya ce an amince da naɗin sabuwar magatakardar ne a taron majalisar dattawan jami’ar karo na 29 da aka gudanar daga ranar Talata 22 ga watan Afrilu zuwa Juma’a 25 ga Afrilu, 2025 a Abuja.

Hajiya Nafisa Barau Suleiman wacce ta yi digirin digirgir (M.A) a harshen Ingilishi a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo (UDUS), Sakkwato, ita ce mace ta farko da ta zamo magatakarda a jami’ar .

Kafin naɗin nata, Hajiya N.B. Suleiman ta zama magatakarda ne bayan kammala wa’adin tsohon magatakardar, Malam Yakubu Anivbassa, a ranar Talata, 4 ga Fabrairu, 2025.

Hajiya Suleiman ta kuma kasance mataimakiyar magatakarda a ofishin shugaban jami’ar, mai kula da harkokin gudanarwa na yau da kullum da makamantansu na ofishin.

Hajiya N.B. Suleiman itace wakiliyar taron jami’a a majalisar gudanarwar jami’ar a halin yanzu.

Sabuwar magatakardar wacce ta taɓa zama babbar Jami’ar Ma’aikata (Establishment Division) kuma Shugaban Ofishin raya ma’aikata, ana sa ran za ta kawo cigaba na gudanarwa da gogewa da zai yi tasiri a kan tafiyar da ofishin ta a halin yanzu.

By ukarofi