
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Ƴan sandan Farin kaya ta DSS, ta yi nasarar ƙwato bindigu ƙirar AK47 guda 50 da alburusai sama da 3,000 da wasu muggan makamai a yayin wani atisaye na musamman a Asaba, Babban Birnin Jihar Delta.
Haka kuma ta kama wani sojan ƙasar Birtaniya mai suna Itsekiri, wanda aka yi zargin sa da sayo makaman ga wani mai suna Collins.
Shaidu daga DSS sun tabbatar da cewa, jami’an hukumar sun kama Major Itsekiri ne a matsayin asalin wanda ake zargi da wasu abokan tafiyarsa da hannu a shigowa da haramtattun makaman, ranar Juma’a.
An kama ƴan tafiyarsa ne a Asaba, yayin da shi kuma aka kama shi a Legas a lokacin da ya ke ƙoƙarin ficewa daga Nijeriya ta jirgin sama.
Ana zargin wasu abokan hamayyar siyasa ne daga mazaɓar Warri da hannu a sayen makaman, lamarin da ya sa ake binciken wani hamshaƙin basaraken gargajiya da hannu a laifin.
