Liverpool ta lashe gasar Firimiya ta ƙasar Ingila karo na 20

Spread the love

Ƙungiyar Liverpool ta sake lashe gasar Firimiya karo na biyu cikin shekaru biyar, inda yanzu haka ta daidaita da Manchester United wajen lashe kofin gasar Ingila sau 20 – mafi yawa a tarihi.

A ranar Lahadi, Liverpool ta doke Tottenham da ci 5-1, wanda ya tabbatar musu da sabon kambun.

Sabon koci Arne Slot ya jagoranci nasarar Liverpool a kakarsa ta farko a Ingila, inda ya zama kocin biyar da ya lashe gasar Firimiya a zangonsa na farko. Kafin shi, Jose Mourinho (Chelsea, 2005), Carlo Ancelotti (Chelsea, 2010), Manuel Pellegrini (Manchester City, 2013) da Antonio Conte (Chelsea, 2017) ne suka taɓa yin haka. Claudio Ranieri (Leicester City, 2016) kuma shi ne kaɗai wanda ya lashe gasar a farkon kakarsa da sabuwar ƙungiya.

By ukarofi