Ku daina ɗora mana laifin gazawarku – Fadar Shugaban Ƙasa ga ƴan adawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi kira ga ƴan ɓangaren adawa da su daina ɗora laifin gazawarsu ga Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ta kuma bayyana cewa, demokraɗiyya tana nan daram a Nijeriya, babu wani yunƙuri na hana ƴancin siyasa ko wani yunƙuri na kafa jam’iyya ɗaya tilo a ƙasar.

A wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan yaɗa labarai ya fitar, gwamnatin ta ce ƙorafe-ƙorafen da wasu ƴan adawa da masu kare haƙƙin ɗan-adam ke yi na cewa ana ƙoƙarin karya demokraɗiyya, batu ne da ba shi da tushe balle makama.

Sanarwar ta bayyana cewa ƴan adawa sun shiga ruɗani ne tun bayan sauya sheƙar da Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, da Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Dakta Ifeanyi Okowa, da wasu manyan ƴan siyasa daga Jihohin Delta da Rivers suka yi zuwa jam’iyyar APC.

Fadar ta musanta zargin cewa ana amfani da tsoro, cin hanci ko tilas wajen karkato ra’ayin masu sauya sheƙar, tana mai cewa ƴancin zaɓin jam’iyya haƙƙi ne na kowane ɗan kasa.

Kazalika, ta ce waɗanda ke kuka da sauya sheƙa suna fatan jam’iyyar APC ta afka rikici ne domin su samu damar cin gajiyar rikicin.

Sanarwar ta jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu ya kasance ɗan rajin demokraɗiyya tun zamanin gwagwarmaya, kuma yana cigaba da gina harsashin tabbatar da demokraɗiyya a Najeriya.

Haka kuma, ta yi kira ga ƴan Nijeriya da su guji jin maganganu marasa tushe daga masu yaɗa ƙarairayi daga ƴan adawa.

A ƙarshe, sanarwar ta yaba wa Shugaba Tinubu da Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Ganduje, bisa ƙoƙarinsu na sa jam’iyyar ta zama abar so da jan hankalin ƴan ƙasa.

By Babaji