Kusancin tsohon ɗan majalisa, Farouk Lawan da ƴan APC ya fara ɗaukar hankalin jama’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Watanni kaɗan bayan fitowarsa daga gidan yari, an ga yadda tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Farouk Lawan kan halarci tarukan APC a ƴan kwanakin nan, lamarin da ya sa ake raɗe-raɗen akwai yiwuwar ya zama ɗan jam’iyyar nan ba da jimawa.

Farouk Lawan ya wakilci mazaɓar Ɓagwai/Shanono ta Jihar Kano a majalisar daga shekarar 1999 zuwa 2015.

An sako shi ne a watan Nuwamban shekarar 2024 bayan shafe shekaru biyar a kurkuku bisa tuhumar sa da laifin hannu a cin-hanci.

Bayan haka ne ya bayyana cewa, a yanzu ne za a buɗe sabon babi game da harkokin siyasarsa, lamarin da ya sa ake ganin sa da wasu jiga-jigan ƴaƴan APC musamman shugabanta na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje akai-akai.

A karon farko da ya je mazaɓarsa bayan fitowarsa daga kurkuku, an gan shi sanye da jar hula da ke nuna alamar goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya ta jam’iyyar NNPP, kana daga bisani aka ga ya sauya akala.

Haka kuma Farouk Lawan shi ne tsohon shugaban kwamitin majalisar kan gyare-gyaren doka a lokacin da ya ke ɗaya daga cikin ƴaƴanta.

By Babaji