Daga MUKHTAR YAKUBU
An rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar ‘yan fim ta KAFIGAN reshen Jihar Kano waɗanda za su jagoranci ƙungiyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.
A daren ranar Asabar 10 ga Janairun nan ne aka yi taron rantsar da sabbin shugabannin a ɗakin taro na Meenat Eɓent Center dake Lodge Road a Unguwar Nassarawa GRA cikin garin Kano.
Taron wanda ya samu halartar dubbun jama’a daga sassa daban-daban na ƙasar nan, an fara shi ne da misalin ƙarfe 7 na dare.
Tun da farko da yake jawabi a wajen taron, Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar Alhaji Ismaila Na’abba Afakallahu ya nuna farin cikinsa a game da yadda ‘yan fim suka karɓi tafiyar wannan ƙungiya wadda a ɗan lokaci daga kafa ta zuwa yanzu an fara ganin ci gaba a game da yadda tafiyar take don haka abu ne da ya kamata mu yi godiya ga Allah bisa nasarorin da muke samu, kuma muna matuƙar godiya da haɗin kai da muke samu, kuma in sha Allahu a matsayin mu na shugabanni za mu ci gaba da tsayin daka don ganin an cimma nasarar da ake buƙata ta kafa ƙungiyar.
Shi ma guda daga cikin jagororin ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Adamu Bello Ability ya bayyana sabuwar ƙungiyar ‘yan fim ta ‘Kannywood Film Industry Guilds Associations ‘(KAFIGAN) a matsayin wata ƙungiya da ta zo domin ta kawo gyara a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood. Inda yake cewa: “Wannan ƙungiyar ‘yan fim ce wadda ta haɗa kowa da kowa, kama daga furodusa, darakta jarumai da sauran masu sana’a a cikin masana’antar Kannywood. Don haka wannan ƙungiya ba ta ware kowa ba, wajen tafiyar ta kowa nata ne.”
Ya ƙara da cewa ” Babbar manufar wannan yunƙuri shi ne samar da daidaito da kuma haɗin kai a tsakanin mutanen da suke cikin masana’antar Kannywood da kuma haɗa ƙarfi waje guda domin tunkarar irin matsalolin da muke ciki, don haka za mu yi duk mai yiwuwa wajen ganin wannan masana’anta tamu ta samu ci gaban da ake buƙata yadda ko da na baya idan suka zo za su ci moriyar ta. Muna fatan waɗannan shugabanni da za a rantsar na reshen Jihar Kano za su yi aikin tuƙuru wajen haɗa kai tare da jawo sauran abokan sana’ar mu cikin wannan tafiya domin mu gudu tare mu tsira tare.”
Bayan kammala jawabin nasa ne aka rantsar da sabbin shugabannin, waɗanda suka hada da; Isah A Isah a matsayin shugaba. Mansurah Isah mataimakiya ta ɗaya, Hannatu Bashir mataimakiya ta biyu, Sani Ahmad Kankarofi Sakatare, da Muhammad Mukhtar Daneji a matsayin Jami’in yaɗa labarai.
Sauran shugabannin sun haɗa da Shu’aibu Idris Lilisco, Muhammad A Bashir, Hafsat Abduhadi, Tage Mustapha Sharif Anwar Abdulhadi Nasidi Alin Baba, Hadiza Musa Maikano, Aminu Ilu Shehu Danbazau Shehu Umar Ibrahim Bala Muhammad Sa’id Dalha Dandano, da kuma Habibu Yaro Haruna.
A lokacin da yake jawabi bayan rantsar da su a matsayin shugabanni, sabon shugaban reshen Jihar Kano Alhaji Isah A Isah, ya yi alƙawarin tafiyar da ƙungiyar bisa gaskiya da riƙon amana, inda ya yi kira da abokan tafiyarsa da aka rantsar da su da su ba shi goyon bayan da ya kamata domin sauke nauyin da aka ɗora musu.
Haka nan ya yi kira ga masu gudanar da harkokin sana’o’in su a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood da su rungumi wannan tafiyar, domin ta su ce gaba ɗaya don haka ya nemi gudunmawar wajen tafiyar da ƙungiyar don a tafi tare a tsira tare.
An dai tashi daga taron wajen ƙarfe goma da rabi na dare tare da karrama wasu muhimman mutane da suke bai wa harkokin matasa da sana’o’i gudunmawa domin ƙarfafawa a gare su.
