Noel: Matashin da ke jinin al’ada duk wata kamar mace

Spread the love

Shafin Al’ajabi ya saba binciko abubuwan da ke ban mamaki, labaran da ke ɗaure kan mutane, tare da buɗe idanu kan halittun Allah da ke wuce hasashen kwakwalwa. A wannan karo, mun kawo muku labarin wani matashi daga ƙasar Philippines wanda rayuwarsa ta cika da sirri mai nauyi, sirrin da ya ɗauki shekaru yana ɓoyewa cikin zuciya.

Noel, wani matashi daga garin Batangas, ya fara fuskantar abin da bai taɓa zato ba tun yana kusan shekara 12. Kowane wata, na tsawon kwanaki, sai ya riƙa zubar da jini kamar yadda mata ke yi a lokacin al’ada. Ba wai ƙananan ɗigo ba ne, sai dai jini mai yawa da ke kawo masa matsananciyar ciwon ciki, damuwa da tsaiko a rayuwa.

Saboda tsoron a yi masa ba’a ko a ɗauke shi da wasa, Noel bai taɓa sanar da kowa ba. Shi da kansa yake sayen audugar mata, yana ɓoyewa a ɗakinsa, yana rayuwa kamar babu wani abu da ke faruwa. Wannan sirri ya zama masa nauyi fiye da dutsen da ke rataye a wuya.

Noel yana aiki a matsayin ma’aikacin hidima a wuraren cin abinci, amma hakan ya ƙara masa wahala. Lokacin da jinin wata-wata ya zo, sai ya riƙa fama da ciwon ciki, canjin yanayi, gajiya da damuwa. Duk da haka sai ya tilasta kansa zuwa aiki, yana ƙoƙarin tsayawa tsayin daka duk da raɗaɗin da ke cin jikinsa.

A hankali rayuwarsa ta fara rugujewa. Ya fara barin aiki, ya ja baya daga soyayya da ƙulla alaƙa da mutane, yana yawan tambayar kansa: “Wa zai yarda da ni idan na faɗa masa gaskiya?” Wannan tunani ya ƙara masa kaɗaici da damuwa.

Bayan dogon lokaci, Noel ya yanke shawarar neman taimakon likita. Nan ne aka gano gaskiyar da ta girgiza shi. Likitoci sun bayyana masa cewa shi mata-maza ne, wato jikinsa na ɗauke da siffofi na namiji tare da wasu sassan ciki da suka yi kama da na mace. A cikinsa akwai wani ƙaramin rami mai kama da mahaifa, wanda ke haifar masa da zubar jinin wata-wata.

Wannan bayani ya ba Noel amsar tambayar da ta dame shi tsawon shekaru. Duk da cewa ba ya magance dukkan matsalolinsa, amma aƙalla ya samu amsar tambayarsa.

Daga baya, Noel ya yanke shawarar bayyana labarinsa a kafafen sada zumunta. Ba wai don neman tausayi ba, sai dai don ya nuna wa duniya cewa akwai abubuwa da dama da muke hukunta mutane a kai ba tare da sanin gaskiyarsu ba. Labarinsa ya ja hankalin jama’a, ya kuma buɗe tattaunawa kan mutunta juna da fahimtar bambancin halitta.

Noel yanzu yana kira ga mutane da su daina hukunta juna cikin gaggawa, su nuna tausayi da kyautatawa, domin kowa na zauke da nasa nauyin da ba a gani da ido. Labarinsa ya zama darasi mai ƙarfi ga duniya cewa rayuwa tana da asirai da dama, kuma dole ne mu koyi zama masu tausayi da fahimta.

Shafin Al’ajabi na ci gaba da kawo muku irin waɗannan labarai masu tayar da hankali, masu karya shingen tunani, tare da tunatar da mu irin ikon Allah da ke bayyana ta hanyoyi daban-daban.

By ukarofi