Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bangaren bankuna a Nijeriya na fuskantar gagarumin sauyi a tsarinsa, yayin da ƙaruwar amfani na’urorin PoS ke ci gaba da rage muhimmancin bankuna.
Sabbin bayanai daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) sun nuna cewa rassan bankuna 229 sun rufe a faɗin ƙasar nan cikin shekara guda, lamarin da ke nuna sauyin ɗabi’ar jama’a zuwa hanyoyin biyan kuɗi ta lantarki domin mu’amalolinsu na yau da kullum.
Bisa bayanan da CBN ya fitar a cikin Financial Sector Statistical Bulletin na shekarar 2024, yawan rassan bankunan ajiya da cibiyoyin kuɗi ya ragu daga 5,373 a 2023 zuwa 5,144 a 2024. Wannan na faruwa ne duk da cewa adadin bankunan da ke da lasisi ya ƙaru daga 33 zuwa 35 a wannan lokaci. ƙididdigar, wadda ta shafi nau’o’in bankuna daban-daban a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, ta nuna yadda harkar banki ke ƙara karkata daga gini zuwa dandamalin fasahar zamani.
Babban abin da ya kawo wannan sauyi shi ne amfani da PoS, wanda ya zama zaɓin farko ga miliyoyin ’yan Nijeriya da a da ke dogara da ɗakunan banki da ATM.
Bayanai sun nuna cewa adadin mu’amalolin PoS ya tashi daga biliyan 9.85 a 2023 zuwa biliyan 13.08 a 2024, wato ƙarin biliyan 3.23, daidai da kusan ƙarin kashi 33 cikin ɗari a shekara guda.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne darajar kuɗin mu’amalolin. Jimillar kuɗin da aka juya ta PoS ta haura ninki biyu, daga tiriliyan N110.35 a 2023 zuwa tiriliyan N223.27 a 2024. Wannan ƙarin tiriliyan N112.93, wato kashi 102 cikin ɗari, na nuna irin rawar da PoS ke takawa yanzu a biyan kuɗi, tura kuɗi, biyan kuɗin data, kuɗin wutar lantarki da kuma cire kuɗi, musamman a yankunan da rassan banki ba su da sauƙin isa.
Duk da cewa ATM na nan ana amfani da su, ci gabansu bai kai na PoS ba. Adadin mu’amalolin ATM ya ƙaru kadan daga biliyan 1.01 zuwa biliyan 1.02, ƙasa da kashi ɗaya cikin ɗari. Darajar kuzin ma ta tashi daga tiriliyan N28.21 zuwa tiriliyan N29.12, ƙarin kusan biliyan N909 kawai, daidai da sama da kashi uku cikin ɗari. Waɗannan alƙaluma na tabbatar da cewa PoS sun wuce ATM da rassan banki wajen zama babbar hanyar mu’amalar kuɗi ga jama’a.
Raguwar rassan banki ba ta yi daidai a ko ina ba. Jihar Legas, wadda ita ce cibiyar kuɗi ta ƙasar nan, ta ci gaba da riƙe mafi yawan rassan banki da guda 1,521 a 2024, duk da ragin rassan 11 daga 1,532 a 2023. Duk da haka, Legas har yanzu ta ninka kowace jiha yawan rassan da take da su.
Jiha mafi shan wahala ita ce Ebonyi, wadda ta rasa rassan banki 89 a shekara guda. Yawan rassan ya faɗi daga 120 zuwa 31, mafi tsananin raguwa a faɗin ƙasar. Oyo ta rasa rassan 26 ta koma 200, yayin da Neja ta rasa 32 daga 108 zuwa 76. Ekiti da Ondo kowacce ta rasa 18, Anambra da Ogun sun rasa takwas-takwas, Kuros Ribas ta rasa biyar, Filato bakwai, yayin da Babban Birnin Tarayya ya rasa tara, daga 400 zuwa 391. Wannan ya nuna cewa rufe bankuna ba ya taƙaita ga karkara kaɗai, har ma yana shafar manyan cibiyoyin kasuwanci.
Sai dai ba ko ina aka samu raguwa ba. Delta ta ƙara rassan shida, Ribas ta ƙara takwas, haka ma Edo, Kaduna da Kano. Katsina ta ƙara uku, Adamawa da Jigawa biyu-biyu, yayin da Kogi ta ƙara guda ɗaya. Masana na ganin wannan na nuna cewa bankuna yanzu suna zabar inda za su bude rassa ne kawai a wuraren da ke da ƙarfin kasuwanci da muhimmanci ta tattalin arziki.
A ƙarshe, bayanan bankin na CBN sun nuna ɓangaren banki na Nijeriya na cikin matsin lamba na daidaitawa da zamani, yayin da fasaha, tsari da canjin ɗabi’ar jama’a ke sauya yadda ake samar da hidimomin kuɗi. Yayin da PoS suka mamaye kasuwanni, unguwanni da bakin hanya a faɗin ƙasar, bankuna na ƙara sake tunani kan kuɗin da ma amfanin ci gaba da riƙe ɗimbin rassan gini.
