Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sabbin alƙaluman kuɗi da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar sun nuna cewa tattalin arzikin ƙasar ya ci gaba da tafiya ne bisa dogaro da tsabar kuɗi a duk tsawon shekarar 2025, inda mafi yawan kuɗin da ke yawo a ƙasar ke ci gaba da kasancewa a waje da tsarin bankuna.
Bincike kan bayanan ya nuna cewa zuwa watan Nuwamba 2025, kuɗin da ke waje da bankuna ya kai naira tiriliyan 4.91 daga cikin jimillar naira tiriliyan 5.26 da ke yawo a ƙasar. Wannan na nufin kusan kashi 93.35 cikin 100 na dukkan kuɗin tsabar da ake da su na hannun jama’a ne, yayin da kashi 6.65 kacal ke cikin bankunan kasuwanci.
Masana tattalin arziƙi na cewa waɗannan alƙaluma sun tabbatar da cewa ɗabi’ar riƙe kuɗi a waje da bankuna ta zama wata al’ada mai zurfi a tsarin kuɗi na Nijeriya, ba wai martani na ɗan lokaci ga tsauraran manufofin da aka taɓa aiwatarwa a baya ba.
Binciken wata-zuwa-wata ya nuna cewa wannan yanayi ya ƙara tsananta ne a ƙarshen shekarar. A watan Oktoba 2025, naira tiriliyan 4.65 daga cikin tiriliyan 5.06 na kudin da ke yawo sun kasance a waje da bankuna, wanda ke wakiltar kashi 91.87 cikin 100. Zuwa watan Nuwamba, adadin kuɗin da kuma kaso cikin ɗari sun ƙara hauhawa, lamarin da ke nuna yadda kudin tsabar ke taruwa yayin da harkokin kasuwanci ke ƙarfi a ƙarshen shekara.
Bayanan CBN sun nuna cewa a duk tsawon shekarar 2025, rabon kuɗin da ke waje da bankuna bai kusan sauka ƙasa da kashi 89 cikin 100 ba. Shekarar ta fara ne a watan Janairu da naira tiriliyan 4.74 a waje da bankuna daga cikin tiriliyan 5.24 da ke yawo, wanda ke nuni da kashi 90.49 cikin 100. A watan Fabrairu an samu kashi 89.62, kafin ya tashi zuwa kashi 91.91 a watan Maris.
Yanayin ya ci gaba da kasancewa mai tsanani a sauran watannin shekarar. Afrilu ya samu kashi 91.09, Mayu ya haura zuwa kashi 92.39, yayin da Yuni da Yuli suka yi shawagi a kusan kashi 89.7. Zuwa Agusta da Satumba, rabon ya sake haura kashi 92 cikin 100, abin da ke kara jaddada yadda tattalin arzikin ƙasar ke dogaro da tsabar kuɗi.
A taƙaice, Nijeriya ta shafe kusan shekaru biyu a jere inda sama da naira tara cikin kowanne naira goma ke yawo ne a waje da tsarin bankuna.
Bayanan sun kuma nuna cewa jimillar kuɗin da ke yawo a ƙasar ta kai naira tiriliyan N5.26 a watan Nuwamba 2025, mafi girman adadi da aka samu a shekarar. Wannan ya biyo bayan karin kudi a hankali daga tiriliyan N5.01 a watan Mayu da kuma tiriliyan N5.23 a Janairu, bayan da ya sauka zuwa tiriliyan N4.92 a watan Agusta da Satumba.
