An sake ɗage shari’ar Kanu Nnamdi zuwa 10 ga Nuwamba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Tarayya a birnin Abuja ta ƙi amincewa da buqatar da lauyoyin Nnamdi Kanu suka gabatar na maida shi gidan gyara hali dake yankin Kuje a Abuja.

An yi ta ce-ce-ku-ce dangane da makomar Kanu wanda aka daɗe ba a ji ɗuriyarsa ba tun bayan watan Yuli.

Lauyoyin da ke kare Kanu, sun yi ta kira da a fito da shugaban ƙungiyar ta IPOB wanda hukumomi suka gaza gabatar da shi a gaban Mai Shari’a Binta Nyako a zama na ƙarshe da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli.

Baya ga qin amincewa da maida Kanu Kuje, mai Shari’a Binta Nyako, ta sake ɗaga shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba mai zuwa don sauraron ƙararsa wanda ya ƙalubalanci cancantar tuhumar da ake masa.

Kanu, wanda ya ke tsare a hannun hukumar DSS tun bayan ɗage sauraron zaman shari’arsa a watan Yuli ya gurfana a gaban mai shari’a Binta Nyako.

A ranar Litinin hukumomin Nijeriya suka yi gyara kan tuhumen da suke masa guda bakwai.

Amma a zaman na ranar Alhamis Kanu ya ƙi amsa aikata laifukan waɗanda suka ƙunshi cin amanar ƙasa da gudanar da ayyukan ta’addanci.

Jami’an tsaro dai sun hana manema labarai da wasu lauyoyi shiga cikin babban ginin kotun da ke a unguwar Central Area na birnin Abuja.