An yi jana’izar shugaban majalisar malamai na JIBWIS reshen Nasarawa

A yau Litinin aka yi jana’izar Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, HQ/Jos reshen jihar Nasarawa, Ustaz Surajo Alhaji Sabo Keffi tare da mutum biyun da Allah Ya karɓi rayuwarsu a wani hadarin mota da ya rutsa da su a jiya Lahadi, wato Asst National Org. Sectatry, Malam Adam Damaturu da kuma matar Al-Hafiz Idris Isa Nasarawa.

An yi jana’izar ne a garin Fataskum, Jihar Yobe a ƙarƙarshin jagorancin Sheikh Sani Yahaya Jingir.

Yayin sallar janazar

Marigayan sun rasu ne a kan hanyarsu ta zuwa wajen Tafsirin Ramadan. Da fatan Allah ya sa Aljanna ta kasance makomarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *