Waɗanne matakai ƙasar Sin ta ɗauka don tabbatar da tsaro a cikin gidanta?

Daga CMG HAUSA

Harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wani jirgin ƙasan fasinjoji a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, babban birnin Najeriya a kwanaki baya, ya girgiza al’ummar duniya sosai. Lamarin da ya fusata ‘yan ƙasar, inda wasu abokaina ke ta tattauna matakan da suka dace a dauka don daƙile ayyukan ‘yan fashi a Najeriya. A ganina, wataƙila za a iya duba wasu matakan da ƙasar Sin ta taba ɗauka don tabbatar da tsaro a cikin gidanta.

Kamfanin ba da shawara na ƙasar Amurka Gallup ya gabatar da wani rahoto dangane da ayyukan shari’a na ƙasashe daban daban a shekarar 2020, inda ya sanya ƙasar Sin a matsayi na 3 cikin wasu ƙasashe da yankuna 144 ta fannin ingancin harkokin shari’a. Abun da ya nuna cewa, ƙasar Sin na cikin ƙasashen da suka fi samun kwanciyar hankali da tsaro a cikin gida a duniya.

Sai dai idan mun waiwayi tsakanin kimanin shekarar 1980 ta 2000, za mu ga cewa yanayin tsaro na ƙasar Sin bai kai na yanzu ba. A lokacin, ana samun ayyukan ‘yan fashin da suke tare hanya, da ɓarayin da suke satan abubuwa sosai a ƙasar Sin. Sai dai ta yaya ƙasar Sin ta yi nasarar daidaita wannan matsala daga bisani?

Akwai dalilai na kai tsaye guda biyu. Na farko shi ne, a dinga daƙile masu aikata laifuka da inganta ayyukan tabbtar da tsaro. Daga shekarar 1983 zuwa ta 2001, jami’an tsaron ƙasar Sin sun gudanar da manyan ayyukan daƙile masu aikata munanan laifuka a kusan ko wace shekara, inda a cikin shekaru 3 na farko kaɗai, ‘yan sandan kasar suka gurfanar da gungun masu aikata laifuka kimanin dubu 197 a gaban kuliya. Sa’an nan hukumomin tsaron ƙasar, sun yi ƙoƙarin kafa tsarin sa ido na kyamarori don tabbatar da tsaro, da inganta fasahohin binciken laifukan da aka aikata. Zuwa shekarar 2021 ‘yan sandan ƙasar Sin sun cimma nasarar kama kashi 99.8% na mutanen da suka aikata laifin kisa. Ban da wannan kuma, yadda aka haramta mallakar bindiga shi ma ya taka muhimmiyar rawa a fannin tabbatar da tsaro a ƙasar ta Sin.

Dalili na biyu da ya sa aka yi nasarar daidaita yanayin tsaro a ƙasar Sin, shi ne ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma mai ɗorewa. Sanin kowa ne, talauci da rashin adalci wasu manyan dalilai guda 2 ne da suke haddasa aikata laifuka. Saboda haka, gwamnatin ƙasar Sin ta yi matukar kokarin raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama’a. Yanzu haka, cikin biranen ƙasar Sin, hukumomi na kokarin gyara wasu ungwanni marasa ci gaba, don samar da sabbin gidaje masu kyau ga mutane marasa karfi. Kana a cikin yankunan karkara, an yi nasarar fid da dukkan manoma daga ƙangin talauci. Ban da haka kuma, an yi ƙoƙarin raya bangaren ilimi, ta yadda aka yi nasarar koya wa ƙarin mutane fasahohin aiki, da ilimi game da dokoki. Duk waɗannan abubuwa sun taimaka sosai wajen rage aikata laifi.

Sa’an nan, baya ga waɗannan matakan da kasar Sin ta ɗauka, akwai wani dalili na tushe da yake tabbtar da tsaro a cikin gidan ƙasar Sin, wanda ya kasance babbar manufar mulki ta jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin, dake rike da ragamar mulki a ƙasar, wato “mai da moriyar jama’a a gaban kome”. A ƙoƙarin ganin an kare rayukan jama’a, duk da mawuyacin halin da ake fuskanta a fannin tattalin arziki sakamakon annobar COVID-19, hukumomin ƙasar Sin na ci gaba da ƙoƙarin killace da kulawa da duk wani mutum da ya kamu da cutar COVID-19. Don tabbatar da moriyar jama’a, a yayin da ƙasar Sin ke rungumar tsarin ciniki na baiwa kasuwa damar yin halinta, tana ci gaba da ba da dimbin tallafi ga mutane marasa ƙarfi don magance komawarsu cikin wani yanayi na fama da talauci. Wannan dalili shi ma ya sa mahukuntan ƙasar Sin ke ɗaukar duk wani matakin da ya shafi tsaro, tattalin arziki, ko kuma zaman al’umma, don hana abkuwar aikata laifi daga tushe.

Duk da waɗannan bayanai da na zayyana, ina fatan ganin mahukuntan Najeriya sun ɗauki matakin da ya cancanta, wanda ya dace da yanayin da ƙasar ke ciki, ta yadda ita ma za ta yi nasarar tabbatar da tsaro a cikin gida. A watan Ramadan mai tsarki da muke ciki, muna rokon Allah Ubangiji da ya ba mu tsaro da kwaciyar hankali a ƙasashenmu da ma duniya baki ɗaya. Amin.

Fassarawa: Bello Wang