An san masu ɗaukar nauyin ta’addanci amma ake kare su, inji tsohon kwamandan sojoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Manjo Janar Ɗanjuma Ali-Keffi (mai ritaya), wanda kwamanda ne na rundunar sojoji a shiyya ta ɗaya a Jihar Kaduna, ya yi ikirarin akwai mutane masu ƙarfin faɗa a ji da ke alaƙa da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci da satar mai a Nijeriya, waɗanda binciken jami’an tsaro ya fallasa su amma kuma aka ƙyale su.

A wata hira da tashar Arise ranar Alhamis, Janar Ali-Keffi, wanda ya taɓa jagorantar atisayen Service Wing (OSW), da ke da alhakin katse hanyoyin ɗaukar nauyin ta’addanci, ya ce akwai binciken da ya bayyana waɗanda ke ɗaukar nauyin ta’addanci da masu kitsawa da waɗanda ke ɗaukar nauyi ƴan Boko Haram har da masu alaƙa da siyasa.

A cewarsa, kamen jagororin ƴan Boko Haram da masu ɗaukar nauyi a tsakanin shekarun 2017 da 2018 ya taimaka wajen rage ƙarfin mayaƙan.

Lamarin da ya sanadin miƙa wuya na dama daga cikinsu da mutuwar jagoransu na wancan lokaci, Abubakar Shekau.

Tsohon sojan ya ƙara da cewa, Nijeriya tana amfana da tallafin leƙen asiri daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Birtaniya da kuma Amurka, inda sakamakon bincikensu ya fallasa asiri amma daga baya ba a ɗauki mataki a kai ba.

Kazalika, ya bayyana cewa, duk da wakilcin hukumomin DSS, DIA, NFIU da ofishin Antoni Janar na Ƙasa a yayin binciken, an sako manyan waɗanda ake zargi da hannun a ciki ba tare da gurfanar da su ba.

By Babaji