Daga DAUDA USMAN a Legas
An shawarci maniyyatan Nijeriya, musamman waɗanda ke shirin zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali a bana, da su guji ɗaukar miyagun ƙwayoyi da sauran haramtattun abubuwa zuwa ƙasar Saudiyya, domin kare mutuncinsu da kuma mutuncin Nijeriya baki ɗaya.
Wannan shawara ta fito ne daga bakin Alhaji Salisu Lale, limamin Masallacin Kamsas Salawatu da ke Gidan Kwali a unguwar Ojota, wanda kuma shi ne sakataren Alhaji Ibrahim Dan Soja, Sarkin ’Yan Gwa-Gwan Jihohi 17 na Nijeriya, tare da kasancewarsa Muƙaddamin ɗarikar ƙadiriyya a Jihar Legas.
Alhaji Salisu Lale ya bayyana hakan ne yayin da yake yi wa wasu daga cikin maniyatan Jihar Legas bankwana kafin tafiyarsu zuwa Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed International Airport da ke Legas domin wucewa ƙasa mai tsarki.
Ya jaddada cewa bai dace ba ga maniyyaci da ke kan hanyar zuwa aikin Hajji ya riƙa sayen haramtattun kaya ko miyagun ƙwayoyi da nufin zuwa kasuwanci da su a Saudiyya domin neman kuɗi.
A cewarsa, irin waɗannan ayyuka na iya jefa mutum cikin matsala tare da ɓata ladar ibadar da ya je yi a ƙasa mai tsarki.
Ya ƙara da cewa, ya zama wajibi maniyata su kasance jakadu nagari na Nijeriya ta hanyar bin dokoki da ƙa’idojin ƙasar Saudiyya, domin hakan ne zai taimaka wajen kare martabarsu da kuma mutuncin ƙasar su.
Alhaji Salisu Lale ya bayyana fatan cewa maniyatan bana za su yi amfani da shawarwarin da aka ba su domin gudanar da ibadarsu cikin nasara da kwanciyar hankali.
Hakazalika, ya yaba da ƙoƙarin Alhaji Ibrahim Dan Soja, Sarkin ’Yan Gwa-Gwan Jihohi 17 na Nijeriya, bisa yadda yake haɗa kan mambobin ƙungiyar tare da ƙoƙarin kawo ci gaba ga ƙungiyar baki ɗaya.
Ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su ci gaba da bai wa shugabansu haɗin kai da goyon baya domin samun nasarar gudanar da ayyukan ƙungiyar.
A ƙarshe, Alhaji Salisu Lale ya nuna damuwarsa kan hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya, yana mai cewa lamarin ya jefa ’yan kasuwar Nijeriya cikin mawuyacin hali.
Sai dai ya bayyana cewa yana ci gaba da yi wa Nijeriya addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa da ci gaba a fannoni daban-daban.
