An tsare na hannun daman Tambuwal kan zargin ɓata sunan matar gwamnan Sokoto

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata kotu a jihar Sakkwato ta bada umarnin tsare wani Shafi’u Umar-Tureta wanda na hannun daman tsohon gwamnan jihar, Aminu Tambuwal ne kan zarginsa da ɓata sunan Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu da matarsa, Hajiya Fatima Aliyu.

Ana zargin Umar ne da yaɗa saƙo a kafar sada zumunta da ya ƙunshi bidiyo da rubutu da nufin ɓata sunan gwamnan da matar tasa.

Acikin bidiyon, an nuna yadda matar gwamnan ke watsa kuɗaɗe a ƙasa da sunan murnar zagayowar shekarar haihuwarta, yayin da shi kuma gwamnan a wani rubutu, wai bai ci jarrabawar kammala makarantar sekandire ba don haka bai iya turanci ba.

Kawo yanzu, Umar-Tureta bai amsa laifin da ake tuhumar sa akai ba duk da kuton ta bada damar a tsare shi.

A ranar 18 ga watan Satumba, 2024 ne za a dawo domin cigaba da sauraron ƙarar.

By Babaji