Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa shugaban masu fafutikar kafar ƙasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai.
Wannan ya biyo bayan hukuncin da Mai Shari’a James Omotosho ya yanke a ranar Alhamis, 20 ga Nuwamba, 2025.
A cewar alƙalin, “wanda aka yanke wa hukuncin bai yi abin da ya dace ba a duk lokacin zaman kotun, yana mai jaddada cewa ya jawo tsaiko a shari’ar.
Ya ƙara da cewa kotun ba za ta yi la’akari da raini da shugaban IPOB ɗin ya yi a kotu yayin da yake yanke hukunci ba.
Omotosho ya ce, “Kotun tana yi wa Kanu rahama ne kawai saboda mun kasance tare da ubangijinmu Yesu Kiristi don mu zama masu rahama. Kanu bai nuna wani nadama ba; yana da girman kai da rashin biyayya. Zan rangwanta masa.
Alƙalin Omotosho ya yanke wasu hukunce-hukunce kamar haka: Dangane da tuhuma ta 3, ya yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin shekaru 20, saboda hukunci na 7 ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 5 ba tare da zaɓin tara ba a duka biyun.
Hukuncin zai gudana a lokaci guda.
Omotosho ya ce dole ne a ajiye Kanu a wurin da ya dace domin yana da wasu halaye masu tsoratarwa, wanda ya nuna su a kotu.
Alkalin ya ƙara da cewa ba za a bar mai laifin ya yi amfani da na’urorin zamani ba, kuma idan dole ne ya yi hakan, dole ne Mai Ba da Shawara kan Tsaron ƙasa ya sa ido sosai a kansa.
Kotun ta ba da umarnin a tsare mai laifin a kowane wuri mai kariya a kowane yanki na ƙasar.
Omotosho ya ƙara ambaton ayar Littafi Mai Tsarki da ke cewa, “Martha Babi na 23 na Littafi Mai Tsarki, inda yake wa’azin rahama.”
Tun da farko, kotun ta yanke wa shugaban ‘yan awaren hukunci bisa zargin da ke da alaƙa da “ta’addanci” bayan shari’ar da aka shafe shekaru ana yi.
Alƙalain da yake shari’ar, Mai Shari’a James Omotosho ya ce masu gabatar da ƙarar sun tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa Nanamdi Kanu.
Tuhume-tuhumen da ake yi wa Kanu sun haɗa da ta’addanci da tunzura jama’a su kashe ‘yan sanda da kasancewa mamba a haramtacciyar ƙungiyar IPOB da gwamnatin Nijeriya ta haramta da kuma yaɗa farfagandar ta’addanci.
Mai Shari’a Omotosho ya ɗage zaman na wani ɗan lokaci inda ya ce zai yanke wa Nnamdi Kanu hukunci idan aka koma nan ba da jimawa ba.
Ana sa ran wannan ya kawo ƙarshen kimanin shekara 10 da aka kwashe ana shari’a, tun bayan da gwamnati ta gurfanar da shi.
Mai shari’ar James Omotosho ya ce zai yanke hukuncin ne a jiya Alhamis bayan Kanu ya gaza kare kansa duk da damar da aka ba shi.
A watan Maris ne Omotosho ya karɓi jagorancin shari’ar, inda ya fara daga farko, bayan jagoran na IPOB ya zargi tsohuwar alƙaliyar da ke shari’ar, Binta Nyako da rashin adalci, sannan ya buƙaci ta tsame kanta daga shari’ar.
Mai shari’a a Omotosho ya bai wa lauyoyin gwamnatin Nijeriya wa’adin kwanakin da za su gabatar da duk tuhume-tuhumensu, da gabatar da shaidu da kammala duk wani ƙorafi da suke da shi.
Babban Lauyan Nijeriya, Adegboyega Awomolo, wanda shi ne jagoran lauyoyin gwamnatin Nijeriya ya kamala gabatar da shaidu da tuhume-tuhume kamar yadda alƙalin ya umarta.
Tawagar gwamnatin tarayya ta kammala gabatar da shaidu da hujjojinta ne a ranar 19 ga watan Yunin 2025.
Daga cikin abubuwan da suka gabatar sun haɗa da bidiyoyi da sautukan da aka naɗa na bayanan Nnamdi Kanu, ciki har da inda yake umurtar mabiyansa su kai farmaki da kuma kashe sojoji da ‘yansandan Nijeriya, da lalata kadarorin gwamnati, da kuma inda yake yi wa mutanen kudu maso gabashin Nijeriya barazana idan suka ƙi yin biyayya ga dokarsa ta zama a gida.
A nata ɓangaren, tawagar lauyoyin Nnamdi Kanu, ƙarƙashin jagorancin tsohon ministan shari’ar Nijeriya Kanu Agabi, daga farko sun gabatar da buƙatar cewa kotu ta zartar da hukuncin cewa babu wani laifi da Kanu ya aikata kuma babu buƙatar ya gurfana a kotu.
Sun buƙaci kotun ta yi watsi da duk wasu tuhume-tuhume da ake yi masa, domin a cewarsu babu wata hujja ta gurfanar da shi.
Sai dai mai shari’a Omotosho ya yi watsi da batun nasu, inda ya ce akwai buƙatar Kanu ya gurfana a kotu domin bayar da bahasi kan wasu shaidu da aka gabatar a kansa.
Daga lokacin ne tsarin tafiyar da shari’ar ya fara tabarɓarewa.
Da farko, Nnamdi Kanu ya kori lauyoyinsa sannan ya ce shi ne zai kare kansa.
Bayan ba shi lokaci domin duba takardun tuhume-tuhumen da ake yi masa da kuma shirya yadda zai kare kansa, a zama na gaba Kanu ya shaida wa kotu cewa babu halasci a tuhume-tuhumen da ake yi masa, saboda haka babu bukatar ya kare kansa.
Kanu ya dage kan cewa dokokin da lauyoyin gwamnati suka dogara da su wajen tuhumarsa tsofaffin ne waɗanda aka soke, saboda haka ya buƙaci alƙali ya sake shi, ya yi tafiyarsa.
Daga nan ne alƙalin ya shaida wa Kanu cewa an wuce matakin yin muhawara kan abubuwan da yake magana a kai, amma ya ce zai yi la’akari da su a lokacin yanke hukunci, sannan ya shawarce shi da ya gabatar da hujjojinsa na kariya daga tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Bayan ɗage shari’a sau shida, inda a duk wannan lokacin mai shari’a Omotosho ya riƙa shaida wa Nnamdi Kanu haɗarin rashin gabatar da hujjojin kare kansa, sai alaƙalin ya yanke hukuncin cewa Kanu ya rasa damar da yake da ita ta kare kansa.
Kwanaki kaɗan bayan haka sai Nnamdi Kanu ya shigar da ƙara a kotun daukaka ƙara yana buƙatar a dakatar da babbar kotun daga shirinta na yanke hukunci har sai ta saurari ƙorafinsa na cewa dokokin da aka dogara da su wajen tuhumarsa tsofaffi ne da aka daina amfani da su.
