An yi garkuwa da tsohon shugaban NLC Takai Shamang a mahaifarsa Biniki da ke ƙaramar hukumar Kaura a Jihar Kaduna.
Shamang, mai shekaru 78, ya kasance tsohon shugaban ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki da iskar gas ta ƙasa, a yanzu ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta ƙasa, tsakanin 1982 zuwa 1989.
Da take tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, ɗiyarsa, Grace Abbin, ta ce an sace mahaifinta mai shekaru 78 a gidansa da ke Biniki, da misalin karfe 8:00 na daren ranar Juma’a. Shamang shi ne shugaba, kuma wanda ya kafa gidauniyar Gantys Aid for Widows, Orphans and Needy Foundation, wadda aka fi sani da GAWON Foundation.
