Badaƙalar biliyan N80.2: EFCC ta gano shirin Yahaya Bello na ficewa daga Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC), ta ce gano shirin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello na ficewa zuwa ƙasar Maroko daga Kamaru sakamakon zargin badaƙalar biliyan N80.2 a kan sa.

Tsohon gwamnan wanda akwai batutuwa 19 na laifuka da ake zargin sa da aikatawa cikin har da badaƙalar kuɗi, zamba cikin aminci da kuma sauya akalan waɗansu kuɗaɗe da adadin su ya kai kimanin Naira biliyan 80.2.

Duk da cewa ya musanta aikata laifukan, gwamnan ya ƙi amincewa a lokuta mabanbanta ya bayyana a gaban Alƙali Emeka Nwite.

A ranar 27 ga watan Yuni ya kamata a ce ya bayyana a babbar kotun tarayya, amma hakan bai kasance ba wanda ya zama karo na biyar da ya ƙi zuwa kotun. Sauran ranakun sun haɗa da; 18 ga watan Afrilu, 23 ga watan Afrilu, 10 ga watan Mayu da kuma 13 ga watan Yuni.

A madadin zuwa kotun, Yahaya Bello ya tura lauyoyinsa kan cewa su nemi a mayar da ƙarar zuwa reshen kotun da ke Lokoja, babban birnin jiharsa.

Sai dai, yayinda ake jiran bayyanarsa a gaban kotu a Abuja ranar 17 ga watan Yuli, wani bayani na sirri ya nuna cewa Yahaya Bello na cikin jadawalin waɗanda ake sanya ido a kansu na kasashen Moroko, Tunisia da Algeriya kasancewar EFCC ta buƙaci kasashen Arewacin Afirka da su sanya shi cikin jadawalin, kamar yadda jaridar ‘The Nation’ ta ruwaito.

By Babaji