Da ƊUMI-ƊUMI: Yadda ƴan majalisa na ɓangaren Fubara da na Wike ke mabambantan zama a Ribas

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ana cigaba da dambarwar siyasa jihar Ribas yayinda ɓangarori biyu na majalisar dokokin jihar ke gudanar da mabanbantan zama a ranar Litinin.

A ranar Lahadi ne ƴan ɓangaren gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ƙarƙashin jagorancin Victor Oko-Jumbo na majalisar, suka gayyaci Emmanuel Frank Fubara domin tantance shi a matsayin wanda za bai wa muƙamin kwamishina kuma ɗaya daga cikin mamba majalisar zartarwa ta jihar.

Sai dai, a gefe guda, ƴan majalisu da ke ɓangaren tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, ƙarƙashin jagoranci Martin Amaewhule za su yi nasu zaman a rana ɗaya da ƴan Fubara. Yayinda da ƴan Fubara ke zamansu a fadar gwamnatin jihar, su kuma ƴan Wike za su yi nasu a ofishin majalisar dake kan hanyar Aba a Fatakwal.

Wannan shi ne karo na farko da ƴan Wike ke gudanar da zaman majalisa tun bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da su a matsayin halastattun mambobin majalisar.

A watan Oktoban 2023 ne aka ƙona ɗakin taron majalisar dokokin jihar dake kan hanyar Moscow a Fatakwal sakamakon wani yunƙurin ƴan majalisu 27 ɓangaren Wike na tsige Fubara.

By Babaji