Gwamnan Zamfara ya sami kyautar Shugaban Ƙasa ta NEAPS

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya sami kyautar NEAPS ta Shugaban ƙasa sabida ayyukan da gwamnatin shi ta assasa kuma ta kammala a cikin shekara guda

Kyautar NEAPS wani sashi ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Kamar yadda wata sanarwar ta fito daga bakin mai magana da yawun Gwamnan Sulaiman Bala Idris, ya shaida cewa an yi wannan bikin bada kyautar ne, ranar Asabar a babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa.

Sanarwar ta shaida Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shi ya bada kyautar ga Gwamna Dauda Lawal a madadin Shugaba Tinubu.

Sanarwar ta cigaba ta nuna cewa sun samu takardar cin kyautar ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Gwamna Dauda Lawal ya nuna farin ciki sosai da wannan kyautar, yace zata zamo wani abin zaburarwa domin cigaba da ayyuka alheri da sukeyi domin cigaban Jihar Zamfara.

By ukarofi