Da ƊUMI-ƊUMI: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori ƙarar shuwagabannin ƙananan hukumomi na ɓangaren Wike

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Kotun ɗaukaka ƙara reshen jihar Ribas, ta kori ƙararraki biyu da shuwagabannin ƙananan hukumomi da ke ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike suka shigar bayan da ta ce ba su cika ƙa’idojin sauronsu ba.

Hon. Enyiada Cookey-Gam da wasu mutum shida suka shigar da su masu ɗuake da lambobi kamar haka; CA/PH/137M/2024 da kuma CA/PH/145M/2024 inda a ciki su ke ƙalubalantar karamar kotu kan hukuncinta na ƙara wa’adin shugabancin majalisar da suka nema.

Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce ƙalubalen nasu basu gamsar da tsare-tsaren doka ba don haka, ta yi watsi da su. Ɗaya daga cikin ƙudurin shi ne batun ƙara wa’adin shugabancin ƙananan hukumomi wanda ƴan majalisu na ɓangaren Nyesom Wike ƙarƙashin jagoranci Martin Amaewhule ke neman a ƙara wata shida ga kantomomi 23 wanda asali zai ƙare ne a watan Yuni.

Kasancewar gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya ƙi amincewa da kuma tabbatar da hakan, sai ƴan majalisun suka yanke miƙa lamarin ga kotu.

Rikicin siyasar jihar ya nuna irin yadda ake gwagwarmaya da kuma samun sauye-sauyen salon siyasa wanda haka ya sa ake samun ɗar-ɗar ga gwamnatin jihar da kuma ƴan ɓangaren tsohon gwamnanta Nyesom Wike.

By Babaji