
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa ya warware batun cewa ya yi murabus daga buga wa ƙungiyar wasan.
Musa bai buga wasa ko ɗaya ba ciki wasannin 7 da Super Eagles ta yi a gasar kofin Nahiyar Afirka da aka buga na wannan shekarar inda ta ƙare a ta biyu.
Ahmed Musa, wanda tsohon ɗan wasan gaba na Leicester City ne, ya buga wasa na ƙarshe daga farkonsa ne wa Super Eagles tun a shekarar 2021, a wani wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya da Nijeriya ta yi da ƙasar Cape Vade wanda ta yi nasara da ci biyu da nema.
Wasan ƙarshe da ya buga wa Nijeriya, shi ne na ƙawance da ya yi na minti bakwai a watan Janairu tsakanin ta Guinea.
Sai dai, a lokacin da ya ke hira da manema labarai bayan wani wasan ƙawance da ya shirya, Musa ya ce “na ɗauki takaitaccen hutu ne daga buga wa Super Eagles, amma ban bar ƙungiyar ba”.
Kazalika, kyaftin ɗin ya kasance ɗan wasa mai zaman kansa tun bayan da aka tsayar da kwantiraginsa a ƙungiyar Sivasspor ta ƙasar Turkiyya.
