Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Faskari Hon, Sama’ila Mu’azu Bawa ya gabatar da wannan ƙudirin a zauren majalisar dokokin inda ya buƙaci gwamnati da ta kawo masu ɗauki na gaggawa.
Bayan gabatar da ƙudirin, majalisar tayi doguwar muhawara, bayan amincewa da ƙudirin sai kakakin majalisar ya umurci akawun majalisar da ya tura wa ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakin da ya dace.
Haka kuma majalisar da amshi rahoto akan dokar sake fasalin wa’adin shugabannin ƙananan hukumomi 34 da ke jihar,daga shugaban kwamitin kula da harkokin mulki na majalisar Hon Salisu Hamza Rinjaye.
Har ila yau, majalisar ta karɓi rahoton akan dokar garambawul ga tsarin shari’a a Jihar Katsina daga shugaban kwamitin kula da harkokin shari’a na majalisar Hon lawal Abdu ƙanƙara.
Bayanin amsar rahotannin guda biyu, majalisar ta yaba wa kwamitocin bisa nuna ƙwarewa wajen gudanar da aikin su. Kakakin majalisar ya bada tabbacin majalisar za ta yi nazari akan rahoton domin amincewa da su.
