Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jarida mai farin jini, Manhaja. Allah ya sa mu amfani juna, amin.
A yau darasin namu mai tsauri ne, don haka zan yi iya mai yuwa don ganin bai kasance rubutun da za a yi wa mummunar fahimta ba.
Kafin mu kai ga darasin namu, bari mu waiwayi abinda littafi mai tsarki Al’ƙur’ani ya faɗa game da auren mace fiye da ɗaya.
Allah mazaukakin Sarki Ya faɗa a cikin littafi mai tsarki, “Ku aura daga abinda ya yi muku daɗi na daga mataye, biyu, ko uku, ko huɗu, Idan kun ji tsoron yin adalci (a tsakanin matayen), to ku auri ɗaya.”
Na tuna wata ƙissa da aka ba mu da ta faru a zamanin Sarkin Musulmi Abubakar na III. An yi wani malami da da yake fatawar cewa, mata tara ne Allah ya halastawa Musulmi. Shi dai wannan malamin ya kafa hujja da kalmar ‘wa’ da ke nuni da ƙari, wato ‘da’ a matsayin dalilin da zai sa a haɗe adadin biyu da uku da huɗu.
Sarkin Musulmin ya ɗauki matakin da ya kamata kan malamin, wanda ba shi ne abinda muke son karkata kai ba, abinda nake son fitarwa, kalaman da suka biyo bayan da Sarkin ya nemi malamin ya janye furuncinsa ya ƙi, shi kuma ya yanke masa hukunci.
ɗaya daga ciki zan maimaita, shin ko maza sun san sharuɗɗan da ya kamata su cika kafin su ƙara aurre?
Wannan dai ita ce maganar da malam bahaushe ya yi fatali da ita, wadda idan zai yi duba da ita, kuma ya yi wa kansa adalci, to da an samu gyara ga yawaitar saki da kuma ƙarin matsalolin da ke gudana a gidajen da ke ɗauke da mata fiye da ɗaya.
Da farko ya kai malam bahaushe, yayin da ka yi yunƙurin ƙara aure, wanda ya kasance babbar sunnah, ka yi duba zuwa ababe kamar haka;
1. Shin menene ƙarfin aljihunka?
Akwai wani hadisi da yake yawan yawo a bakunan mutane, wanda wasu daga cikin malamai sun ce isnadinsa mai rauni ne, duk da cewa, ban yi dogon bincike kai ba, hadisin wanda aka ce wani bawan Allah ya je wurin ma’aikin Allah, ya sanar da shi talauci ya masa yawa, sai Manzon Rahma ya ba shi umurnin ya je ya ƙara aure.
Da wannan suke cewa ƙarin aure, maganin talauci ne, don haka da sun ɗan sami wani abu da za su ciyar da iyalansu da ke cikin mawucin hali, sai ya tara shi ya ƙaro wata mata.
Idan muka ɗauki rayuwar wasu, za mu iya cewa, Allah bai kasance azallumin sarki ba, don haka ba za mu iya amincewa da cewa, ƙarin auren da za su yi na daga cikin umurnin ubangijin da suke iƙirari ba.
Mutumin da yake zaune da matar shi, da ‘ya’yanshi, ba abinda yake ba su, ko idan ya samo ma sai matar ta yi ‘yan dubaru, sannan za a ci, ba dai don an ƙoshi ba. ‘Ya’yanka na yawon gari, don samun ɗan abinda za su cike giɓin da iyayensa suka kasa cika masa.
Ba ka damu da inda suke zuwa ba, ko mai suke yi don su samu abinda suka ci ba, kawai dai ka zama silar zuwansu duniya, kuma tun a ɗaukar cikin nasu ne ka gama masu aikinsu. Duk wata hidima kan uwar yake. Ba ka ba su tarbiyya ba, wadda wajibi ce.
To da wannan ne za ka iya cewa ƙarin aure alheri ne gare ka?
Za mu ci gaba a mako mai zuwa insha Allah.
