Yahudawa sun dira kan Goldenberg

Spread the love

Yaƙin da Isra’ila ke yi kan Gaza ba iya nan ya tsaya ba don duk inda Israi’ilawa ko Yahudawa kan dau matsaya kan yaƙin ta hanyar tsananin mara baya ga murƙushe Gazawa da a ke yi amma wasu na nuna tausayi. Harriet Goldenberg ‘yar ƙungiyar Yahudawa ne da ke Birtaniya da a ka dakatar da ita daga ƙungiyar duk da ta na babban matsayi don nuna ɓacin ran ta ga yadda a ke kashe Falasɗinawa a Gaza. Yanzu haka ƙungiyar Yahudawan ta ƙaddamar da buncike kan wasu ‘yan ƙungiyar 36 da su ka sanya hannu kan wasiƙar nuna damuwa ga zubar da jinin Falasɗinawa. An wallafa wasiƙar ta su a jaridar FINANCIAL TIMES. Waɗanda lamarin ya shafa sun ce ba za su kawar da ido kan yadda a ke kashe rayuka da lalata dukiyoyi a Gaza ba. Wannan a fili ya nuna ba a taruwa a zama daya ga aikata zalunci. In an tuna kwanakin baya ma Isra’ila ta dau irin wannan mataki ga wasu dakarun ta da ke kin jinin yaƙin. Direbobi masu aiki da waɗanda ke jiran maye gurbi da su ka sa hannu kan takardar buƙatar dawo da sauran fursunonin Isra’ila da ke hannun Hamas za su rasa aiki ko ma sun rasa aikin.

Waɗannan direbobin kimanin 1000 sun rantaba hannu kan takardar da a ka wallafa a jaridu da ke buƙatar a tsagaita yaƙi don hakan ya ba da damar dawo da fursunoni cikin salama.

Direbobin na ganin dagewa kan yaƙi ba zai taimaka ba sai ma jefa rayuwar fursnonin a barazana da ma asarar rayukan sojojin Isra’ila da waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.

Direbobin sun ce yaƙin bai shafi tsaro ba sai dai kare muradun siyasa da na kashin kai. Ma’ana gwamnatin na amfani da damar don cimma muradun siyasa.

Tuni Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya mara baya ga korar duk direbobin da su ka sanya hannu daga aiki. Don haka ɗaukar matakin na ƙungiyar Yahudawa a Birtaniya ba abun mamaki ba ne. Hatta ƙasashen mu na Afurka na takatsantsan ga mara baya kai tsaye ga Falasɗinawa don gudun abun da hakan zai jawo na illata dangantaka da Isra’ila da gaggan magoya bayan ta na yammacin duniya. Gwamnatin Donald Trump ta yi wa Afurka ta kudu barazana don yadda ta kai ƙarar Isra’ila kotun duniya da zargin kisan kare dangi ga Falasɗinawa. In za a tuna Amurka a zamanin mulkin tsohon shugaba Joe Biden ta yi ta hawa kujerar na ƙi a kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin Duniya duk lokacin da a ka kawo buƙatar jefa kuri’ar tilasta Isra’ila ta dakatar da yaƙin Gaza. Tsohon sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ya yi suna ne don tafiye-tafiye da riƙa yi gabar ta tsakiya kan yaƙin Gaza duk da ba wata gagarumar nasara da a ka cimma. Najeriya na daga ƙasashen da su ka dau matsayin tsaka-tsaki kan yakin na Gaza amma da buƙatar a samu sulhu don tsaida zubar da jini. Ofisoshin jakadancin Falasɗinawa a Abuja na gudanar da lamuran sa ba wata tsangwama a zahiri. Za mu tuna irin kamfen ɗin neman goyon baya da jakadan Falasɗinu a Nijeriya Abdullah Shawesh ya ke yi. Jakadan Falasɗinawa a Nijeriya Abdullah Shawesh ya ce cikin waɗanda ke gwagwarmayar kwatowa Falasɗinawan haƙƙin su akwai mabiya addinin Kirista da ma Yahudawa.

Jakadan ya ce duk mai tausayi a zuciyar sa zai marawa muradin Falasɗinawan na samun ƙasar kan su daga mamayar Isra’ila.

Shawesh ya zayyana gwagwarmayar da su ke yi ta neman kwatar ‘yanci ce ba faɗan addini ba ne kamar yadda ya ce musamman wasu mabiya addinin kirista a Nijeriya ke ɗaukar Falasɗinawa a matsayin su na Larabawa duk Musulmi ne alhali su na da mabiya addinin Kirista don cikin hare-haren Isra’ila ma ta ruguza wata tsohuwar majami’a mai tarihi a Gaza.

Shawesh ya ƙara da cewa kamar yanda ƙasashen Afurka su ka yi gwagwarmayar samun ‘yanci daga ‘yan mulkin mallaka, hakanan Falasɗinawa ke yunƙurin samun ‘yanci da ya ce sun rasa tun 1948.

Jakadan ya ce duk kayan agajin da a ke shigowa da shi Gaza daga mashigar Rafa ta Masar ba su fi biyan buƙatar kashi 3% na jama’ar Gaza ba.

Shawesh ya ce Nijeriya na da gagarumar gudunmawar da za ta bayar wajen ciccibar neman ‘yancin Falasɗinawa ya na mai godewa ‘yan Nijeriya da irin goyon bayan da su ke ba wa ƙasar sa.

Da a ka tambaye shi ko Hamas ba ‘yan bindiga ne masu saba doka da oda ba?

Jakadan ya ce gasawa Falasɗinawa aya a hannu ya kawo kafuwar Hamas a 1987 inda ba ƙungiyar gabanin nan tun mamaye yankin Falasɗinawa.

Sakataren ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya
reshen arewa ta tsakiya Pastor Simon AS Dolly ya ce nuna tsana ga Falasɗinawa don bambancin addini ba daidai ba ne.

Haƙiƙa tattaunawa da ma muhawara mai zafi kan halin da a ke ciki a Gaza na daga manyan darussa da ‘yan Nijeriya ke wuni su tashi da shi inda wasu ra’ayin su kan zo iri ɗaya wasu kuma su yi harshen damo.

Batun komawa tattaunawa a Katar don sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta bai yi harshe ba tukun yayin da a kusan kullum sai sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa a Gaza.

Harin da Isra’ila ta kai kan Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 17 da lalata kayan aiki.

Harin dai ya auna motocin buldoza da a ke amfani da su wajen kawar da ruguzazzun gine-gine ko ceto mutanen da gine-gine su ka danne bayan hare-haren bom.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya zanta da shugaban Amurka Donald Trump ta wayar tarho inda daga bisani ya aiyana shirin kai ziyara Washington.

Shugaba Trump ya fito a kafar sa ta yanar gizo TRUTH SOCIAL ya na mai ba da labarin zantawar da cewa ta tabo batun Iran da harkokin kasauwanci.

Isra’ila ta ce ta kai hari ne don wargaza motocin na buldoza da zargin Hamas na amfani da su wajen bunne nakiyoyi da tona ramukan ƙarƙashin kasa.

Wani harin Isra’ila na daban ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 2 a kasar Lebanon da ke da Hezbollah mai marawa Hamas baya.

ƙungiyar Hezbollah a Lebanon ta ce sam ba za ta amince da kwance damarar yaƙin ta ba don duk matsin lamba.

Shugaban ƙungiyar da Iran ke marawa baya Naim ƙassem ne ya bayyana haka a jawabin da a ka yayata ta kafar talabijin.

Wannan na zuwa ne yayin da Amurka ke matsawa gwamnatin Lebanon ta Joseph Aoun ta tilasta Hezbollah ta miƙa makaman ta.

Hezbollah wacce hare-haren Isra’ila ya ragewa ƙarfi ta rasa shugaban ta mai dogon zamani Hassan Nasrallah a harin samaniya na Isra’ila.

ƙungiyar dai ta Hezbollah na da tasiri aiunun a siyasar Lebanon kuma ita ke samar da shugaban majalisar dokokin ƙasar.

Ba mamaki rashin janyewar Isra’ila gaba ɗaya daga kudancin Lebanon a yarjejeniyar tsagaita wuta a Nuwambar bara ya sa Hezbollah cigaba da riƙe makaman ta.

Har yanzu Isra’ila kan kai hare-hare cikin Lebanon da sunan farautar mayaƙan Hezbollah.

Kammalawa;

Haka nauyi ya rataya kan duniya musamman ƙasashen Larabawa wajen tsayin dakatar dakatar da zubar da jini a Gaza. Daga fara fitinar ranar 7 ga Oktobar 2023 Isra’ila ta kashe fiye da Falasɗinawa 51,000 a Gaza. Duk mazaunin Gaza ma ba ya tunanin zai wuni ko tashi washegari da rai. Idan an yarda Gazawa mutanene kamar kowa to ya dace a kai mu su dauko ta kowanne fanni don ceto sauran jama’ar su da ke raye a cikin ruguzazzun gidaje da sansanoni.

By ukarofi