Gwamnatin Birtaniya ta barranta daga sojan da aka kama bisa safarar makamai a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Laraba ne Babbar Hukumar ƙasar Ingila ta ƙaryata rahoton da ke zargin wani jami’in soja daga cikin jami’an rundunar sojojinta ya na da hannu a sayen haramtattun makamai a Nijeriya.

A wani saƙo da Kakakin hukumar ya fitar, ya ce mutumin da aka kama, ba ya aiki tare da rundunar sojojin ƙasar a halin yanzu.

Rahotanni sun bayyana cewa, a baya ya kasance ya na aiki da reshe na biyu na rundunar a matsayin ƙaramin soja, kana daga bisani aka sallame shi.

Sanarwar ta kuma ce, hukumar ba za ta bada ƙarin bayani game da mutumin ba la’akari da haramcin hakan da dokar ƙasar ta yi.

A ƴan kwanakin nan ne gidajen jaridu suka ruwaito cewa an kama wani baturen soja da hannu a sayen makamai da safarar su ta haramtattun hanyoyi a yankin Neja-Delta.

Jami’an ƴan sandan farin kaya sun daƙile mummunan aikin ne a ranar Juma’a, inda suka yi nasarar kama wanda ya ke raba makaman, a wani samame da suka kai kusa da birnin Asaba dake Jihar Delta.

A nan ne suka yi nasarar ƙwato bindigu ƙirar AK47 guda 50 da wasu alburusai 3,000 gami da wasu muggan makamai.

Lamarin da ya yi sanadin kama tsohon jami’in a lokacin da ya yi ƙoƙarin ficewa daga Nijeriya a Legas.

Haka kuma masu-ruwa-da-tsaki a yankin Neja-Delta sun nemi Babbar Hukumar Birtaniyan da ta gudanar da bincike akan jami’in da waɗanda ke taimaka masa da kuma gurfanar da su don su fuskanci hukuncin doka.

By Babaji