
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh, ya ce hukumar ta shirye tsaf wajen fara jigilar zangon farko na alhazan shekarar 2025.
Za a fara ɗibar alhazan ne zuwa ƙasa mai tsarki a ranar 9 ga watan Mayu, 2025.
Farfesa Saleh ya bayyana hakan ne a yayin wani zama da masu-ruwa-da-tsaki kan harkokin da suka shafi kula da tsare-tsaren kuɗaɗen mahajjatan da gudanarwasu.
A gudanar da zaman ne, wanda NAHCON da Cibiyar kula da harkokin aikin hajjin Nijeriya da HIN gami da haɗin-gwiwar bankin Ja’iz suka shirya.
Ya ce, Gwamnatin Tarayya ta zaɓi kamfanonin jiragen sama huɗu da za su yi aikin jigilar alhazan Nijeriya guda 40,000 da kuma sama da jami’an gudanarwa guda 14,000.
Ya yi kira ga masu-ruwa-da-tsakin da su haɗe kai wajen sauke nauyin da aka ɗora musu cikin inganci gami da tabbatar da walwalar mahajjatan domin cimma nasara.
Ya kuma yi godiya ga Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima bisa goyon baya da gudunmawa da suka bayar wajen warware matsalolin da aka fuskanta na ƙalubalen aikin hajjin 2025.
