Nijeriya za ta karɓi baƙuncin gasar karatun Alqur’ani ta duniya a karon farko

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Masana Alqur’ani daga ƙasashe 20 ne zasu shiga gasar karatun Alqur’ani ta duniya kuma ta farko a Najeriya wanda tsohon ɗan majalissar wakilai mai wakiltar mazabar Bassa da Jos ta Arewa a Jihar Filato Honourable Muhammad Adam Alkali OON ya ɗauki nauyin shiryawa.

Gasar wadda za ta gudanaa a watan Agustan wannan shekarar, za a fara ta ne a birnin Jos Jihar Filato sannan a kammala a babban birnin tarayya Abuja.

A lokacin gagarumin taron ƙaddamar da kwamitocin shirye shiryen gudanar da gasar ta duniya, wanda gwanayen Qur’ani daga faɗin ƙasar nan suka halarta, Honourable Alƙali yace tuni an sanar da
cibiyar bunƙasa karatun addinin musulumchi ta Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo ta Sokoto ta goyi bayan ƙudirin.

Yace gasar nada nufin haɓaka harkokin addinin Musulunchi da haɗin kan Musulmi, yana mai bayyana mahimmancin karanta Alqur’ani mai girma wanda shine babban malamin dake wanke zuciya da samar da shiriya ga al’ummar Musulmi.

Da yake alƙawarin cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, honourable Alkali ya bada misalin yadda wani bawan Allah yayi ƙoƙarin shirya gasar karatun Alqur’ani ta duniya amma ba a samu nasara ba saboda wasu ƙalubale da aka fuskanta.

A jawabin sa, shugaban kwamitin shirye shirye Gwani Sadiq Zamfara ya yi bayanin irin ayyukan da kwamitin ya gudanar da nufin ganin an samu nasarar gudanar da gasar ba tare da matsala ba, sannan ya yi godiya ga wanda ya ɗauki nauyin shirya gasar.

Ƙasashen da ake tsammanin zasu halarchi gasar sun haɗa da Kamaru da Ghana da Chadi da Senegal da Kenya da Tanzania da Mauritania da Masar da Morocco da Libya da Algeria da Saudiya da Kuwait da Qatar da Malaysia da Ingila da Kuwait da Hadaɗɗiyar Daular Larabawa da Amurka.

Kamar yadda ɗaya daga cikin yan kwamitin shirye shirye Muhammadu Bashir ya sanar ko wace ƙasa za ta zo da mahalarta gasar maza da mata da hukumomin su.

By ukarofi