An yi kira ga ‘yan siyasa a Katsina su guji cin mutuncin juna a yaƙin neman zaɓe

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An yi kira ga ‘yan siyasa a Jihar Katsina da su guji cin mutuncin junan su gabanin fara yaƙin neman zaɓe na 2027.

Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua,Kwamred Mannir Suleiman ya yi wannan kira a Katsina a wata hira da manema labarai.

Kwamred Suleiman ya nuna damuwarsa a yadda kwanaki kaɗan masu zuwa za a fara fita yaƙin neman zabe amma har an fara fitowa kafafen sadarwa ana musayar yawu wanda haka ka iya kawo rigingimu a tsakin su.

Yakamata ‘yan siyasa su san cewa duk wannan yunƙuri da suke yi kan neman kujerar mulki, domin al’ummar Jihar Katsina su ke yi don haka dole su mutunta juna tare da bin ƙa’idojin tafiyar da yaƙin zaɓe kamar yadda hukumar zaɓe ta nada,”Kwamred Suleiman ya ce.

Ya yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa kafa dokar hana ƙauranci da bangar siyasa a Jihar wanda a cewar sa zai taimaka wajen tsafatace gudanar da yaƙin neman zaɓen da gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Kwamred Suleiman ya shawarci gwamnan da ya yi baji ba gani wajen tabbatar da doka ta yi aiki musamman ga ‘yan bangar siyasa da suka addabi manyan ‘yan siyasa musamman masu riƙe da muƙamin gwamnati.

Ya yaba wa gwamna da jami’an tsaro kan yadda suka tashi tsaye wajen yaƙi da ƙauranci da masu sha da safarar miyagun ƙwayoyi a mayan biranen jihar.

” Babu shakka manyan biranen Jihar ya zama matattara na waɗannan miyagun mutane, domin haka ina kira ga mai girma gwamna da jami’an tsaro su cigaba da irin wannan yunƙuri domin ganin alumma ta sami natsuwa.

Kwamred Suleiman ya jaddada goyon bayan ƙungiyar haɗin kan Funtua kan manufofi,tsare tsare da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Dikko Raɗɗa ke aiwatarwa a fadin jihar.

By ukarofi