An zargi Shugabar Hukumar FCC da sayar da guraben aiki a ma’aikatun Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamishinonin Hukumar (FCC) sun zargi shugabar hukumar Farida Dankaka da “sayar da guraben ayyukan yi” a ma’aikatu da hukumomin tarayya (MDAs).

Kwamishinonin sun yi wannan zargin ne a lokacin da kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai ke binciken MDAs da jami’an tsaro da manyan makarantu kan badaƙalar ayyukan yi a Abuja.

Kwamishinonin FCC da suka yi zargin sun haɗa da Abdulrasaq Adeoye (Osun), James Dan’iya (Kwara), Abdulwasiu Bawan-Allah (Lagos), Moses Anaughe (Delta), Mamman Alakayi (Nasarawa), da dai sauransu.

Kwamishinonin sun kuma yi zargin cewa Madam Ɗankaka ta haxa baki da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) don dakatar da wani koke da aka rubuta akanta kan badaƙalar aikin da kwamishinonin suka rubuta.

“Mun roƙi EFCC da ta bincike ta, amma abin takaicin mu ba a yi komai ba. Masu neman aikin suna biyan daga Naira 750,000, har Naira miliyan 7, ya danganta da ma’aikata, hukuma ko cibiyar da ake neman ayyukan.

“Ana tura kuɗaɗen daga asusu daban-daban zuwa babban asusun bankin Access,” kamar yadda suka shaida wa kwamitin.

Kwamishinonin sun yi zargin cewa shugabar ta kan ɗauke kanta daga wata hukuma mai riba zuwa wata.

A martanin da ta mayar dangane da yawaitar zarge-zargen, Madam Dankaka ta ce, “Idan ka yaƙi cin hanci da rashawa, cin hanci da rashawa zai yaƙe ka.

Shugabar FCC ta ƙara da cewa, “Ban zo neman kuɗi ba sai don in yi wa qasata hidima. Abin da wasun su ke nema shi ne kuɗi. Kafin in zo nan, na yi kuɗi na. Wasu daga cikinsu suna da dalilansu na kai mini hari.

“Misali, kwamishinan Osun yana ofishina kullum. Abin da suke zargina da shi ba gaskiya ba ne.”

Madam Dankaka ta ce kafin ta shiga ofis a watan Yulin 2020, dukkan kwamishinonin suna “sayar da ayyukan yi,” ta qara da cewa ƙin shiga cikin badaƙalar ya sa suka fusata da ita.

A cewarta, alal misali, kwamishinan da ke wakiltar Osun ya sayi wata kadara kuma ya shaida wa mutumin cewa zai biya da guraben aiki.

A cewarta, hakan ya sanya ta aike wa MDAs cewa kada su girmama duk wata takarda daga kwamishinonin idan har ba su ga sa hannun ta ba.

Shugabar hukumar ta FCC ta ce ta ki amincewa da tayin nasu na sasantawa, inda ta ƙara da cewa ita ce za ta kasance mutum na qarshe da zai sayar da ayyukan yi, kuma kwamishinonin na da hannu a yakin neman zaɓe a kafafen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta.

Dangane da batun EFCC kuwa ta ce hukumar na son ɗaukar ma’aikata ne kuma ta samu amincewar ta, inda ta ce babu wani lokaci da ta yi sulhu da su.

Shugaban kwamitin majalisar, Gagdi Yusuf, ya ce ‘yan majalisar ba za su shiga harkokin siyasar kowace hukuma ba.

“Za mu yi aikinmu, kuma za a yi adalci,” in ji Mista Gagdi.

Ya tambayi dalilin da ya sa za a yi zargin vacewar takardun da suka shafi ayyukan hukumar ta fuskar ɗaukar aiki.