Ana fuskantar ƙarancin fetur yayin da ‘yan kasuwa suka ƙara farashin defo zuwa N1,350 kowace lita

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Akwai yiwuwar a sake fuskantar ƙarancin man fetur, bayan da ‘yan kasuwar da ke shigo da fetur suka sanar da ƙarin farashin lita a defo zuwa kusan N1,350.

Wannan mataki na iya tilasta wa gidajen mai ƙara farashin da suke sayar wa jama’a, tare da haddasa cinkoso a wasu tashoshin mai matuƙar ba a samu wadatuwarsa ba.

Rahotanni sun bayyana cewa masana’antu tuni suka riga suka sanar da ‘yan kasuwa batun sabon farashin wanda ake sa ran zai fara aiki daga ranar 17 ga Yuli, lamarin da zai tilasta wa gidajen mai ƙara farashi a faɗin ƙasar.

Ana ganin wannan ci-gaba a matsayin abin da zai sake jefa al’umma cikin matsi akan wanda ake ciki na tsadar rayuwa a sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

By Babaji

Leave a Reply