Ana sa ran sama da mutane 5,000 za su halacci taron bunƙasa ayyukan kwamfuta na Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Shugaban riƙon na babban taron nazarin sarrafa ayyukan kwamfuta na Kano, wato Kano Digital Innovation Network (KDIN) Abdulsalam Abdulrashid Hamza Maiturare, ya bayyana cewa ana shirin gudanar da babban taron sarrafa ayyukan kwamfuta, karo na biyu na wannan shekarar ta 2025, wanda za a yi a Kano daga ranar 22 zuwa 26 ga Satumba, ya kwatanta taron a matsayin “Mafi muhimmanci a Arewacin Najeriya.”

Maiturare ya bayyana cewa taron zai ƙarfafa matsayin Kano a matsayin cibiyar ƙirƙire ƙirƙire ta zamani a Arewa da yankin Sahel, bayan nasarorin taron dijital Kano na farko da ya jawo fiye da mahalarta 2,000 daga ko ina a Najeriya da na duniya. Wannan karo ana sa ran samun mahalarta sama da 5,000 ciki har da baƙi daga ƙasashen Afirka ta Kudu, Kanada, Amurka, Kenya da Zimbabwe.

Taken taron na bana shi ne “Ɗorewar tattalin arziki: Magance hada hadar kuɗi, tsaron abinci, ƙalubalen virane da tattalin arzikin kore a Najeriya.”

Taron zai haɗa jama’a daban-daban kamar masu sha’awar ƙirƙire ƙirƙire, masana fasahar sadarwa, ƴan kasuwa, hukumomin gwamnati da matasa. Maiturare ya ce shirin zai ƙunshi jawaban manyan baƙi, tattaunawa kan manufofi, nuna sabbin fasahohi, damar haɗin gwiwa a hanyoyin cigaba tsakanin jama’a da masu zaman kansu da na ƙasashen waje.

Ana sa ran manyan baƙi kamar mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima a matsayin baƙo na musamman da gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin babban mai masaukin baƙi.

Taron zai samu haɗin gwiwa daga gwamnati, ma’aikatu da ƙungiyoyi irin su Arewa Consultative Forum, FinTech NGR, SparkLab, da sauran su.

Kazalika, za a ƙaddamar da shirye-shirye da dama domin bunƙasa ababen more rayuwa, haɗin kai tsakanin ƙasashe, da bunƙasa matasa da mata a ɓangaren fasahar sadarwa.

Maiturare ya ce wannan taro zai taimaka wajen ƙara shigar jama’a cikin harkokin kuɗi ta hanyar amfani da Fasahar FinTech, bunƙasa tsaron abinci ta hanyar sabbin fasahohi na gona, horar da mata da matasa kan ƙwarewar fasahar sadarwa da samar da sabbin ayyuka a birane don bunƙasa tattalin arzikin kore na Kano.

Ya shawarci waɗanda ke sha’awar halarta su ziyarci gidan yanar gizon Kano Digital Innovation Network (KDIN) a www.digitalkano.ng don yin rijista da samun ƙarin bayani.

By ukarofi