Majalisar Wakilai ta gayyaci kamfanonin DisCos 11 kan bashin tiriliyan N2.6

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamitin Asusun Ƙasa na Majalisar Wakilai ya gayyaci kamfanonin raba wutar lantarki (DisCos) guda 11 bisa bashin da asusun tarayya yake bin su.

A ranar Laraba yayin zaman majalisar aka tattauna batun sakamakon bincike ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisa Bamidele Salami bayan gano haramtattun ayyuka a fannin lantarkin Nijeriya a rahoton da Odita Janar ya fitar na 2021.

Darakta Manaja na Kamfanin Kula da Kasuwancin Lantarki a Nijeriya (NBET), Johnson Akinnawo ya tabbatar da cewa an gabatar da takardun basusuka ne a gaban kwamitin domin ɗaukar matakan da suka dace a kai.

A cewar rahoton NBET, zuwa ranar 30 ga watan Satumban 2020, ana bin kamfanonin DisCos guda 11 jimillar kuɗi da adadinsa ya kai Naira tiriliyan 2.6

Ga yadda suke dalla-dalla, kamar yadda jaridar NewsPointNigeria ta ruwaito:
Abuja Disco – biliyan ₦330.4
Ibadan Disco – biliyan ₦325.7

Ikeja Disco – biliyan ₦310
Kaduna Disco – biliyan ₦277.7

Enugu Disco – biliyan ₦258.3
Port Harcourt Disco – biliyan ₦239.7

Benin Disco – biliyan ₦233.2

Eko Disco – biliyan ₦231
Kano Disco – biliyan ₦211.7

Jos Disco – biliyan ₦161.7

Yola Disco – biliyan ₦107.4

Rahoton oditan ya kuma bankaɗo wasu ayyukan rashin gaskiya a kamfanonin, lamarin da ya sa aka gudanar da bincike tare da gano kurakurai da dama a harkar gudanar da fannin lantarki a Nijeriya.

Daga ciki akwai kuɗaɗe kamar haka:

Biliyan ₦30 na bashi da NBET ba ta karɓa daga ƴan kasuwar fannin ba.

Miliyan ₦549 na cajis a NBET.

Biliyan ₦100 da aka biya kamfanonin DisCos na lantarkin da ba su isar wa rumbun lantarki na ƙasa ba.

Biliyan ₦26 da ake bin kamfanonin waje na lantarkin da aka raba musu a Togo, Benin, da Nijar.

Biliyan ₦166 da DisCos ba su shigar wa Hukumar Gudanarwar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ba a matsayin mafi ƙarancin abinda aka ɗora musu.

Sai kuma biliyan ₦2.7 na wasu takardun basusukan kamfanoni sha ɗayan da ba su biya ba.

By Babaji