Jakadan Nijeriya a Kamaru, Ambasada Coker ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatar Harkokin Waje ta sanar da rasuwar Ambasada Taofik Obasanjo Coker, wanda shi ne Jakadan Nijeriya a Buea na Jamhuriyar Kamaru.

A sanarwar da Kakakin ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa ya fitar, Ambasada Coker ya rasu ne a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025 bayan fama da wani gajeren rashin lafiya.

Marigayin ya kasance mai jajircewa akan harkokin difulomasiyya da sadaukarwa wajen yi wa ƙasa hidima, wanda ya wakilci Nijeriya bisa kishi da nuna ƙwarewarsa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, rashinsa zai haifar da babban giɓi ga ɗaukacin ƴan difulomasiyya da ma Nijeriya baki ɗaya.

Gabannin ba shi muƙamin a matsayin jakada a Kamaru, Coker ya yi wa Nijeriya hidima a Conakry, Guinea da Shanghai a Chana.

Ma’aikatar ta kuma miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, abokan aiki, ƴan uwa da abokan arziƙi, tana mai tabbatar musu da samun addu’o’i da agajin gwamnatin tarayya a yayin lokacin jimamin.

By Babaji