Tsaro: Muƙaddashin Gwamnan Katsina ya gana da Babban Hafsan Sojojin Nijeriya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Muƙaddashin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Farouk Lawal Joɓe, ya gana da Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa, a Abuja domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalar ƙaruwar ta’addancin a jihar.

Wannan ziyarar ya biyo bayan mummunar hari da ƴan bindiga suka kai a wani masallaci da ke unguwar Mantau a ƙaramar hukumar Malumfashi inda suka kashe mutane 32.

Bayyana wannan aikata wannan ta’addanci da ƴan bindigan suka aikata sun cigaba da kai hare hare a wasu sassan kudancin jihar inda nan ma an rasa rayuka da dukiyar al’ummar yankin.

Malam Joɓe ya bayyana wa Janar Christopher irin illar da matsalar tsaro ke yi ga rayuwar al’ummomin karkara, musamman asarar rayuka, dukiya da kuma rushewar harkokin noma a jihar.

Ya buƙaci ƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin Katsina da rundunar sojoji domin kawo ƙarshen lamarin.

A nasa ɓangaren, Janar Musa ya tabbatar da cewa rundunar sojoji za ta ƙara ƙaimi domin tabbatar da tsaro a Jihar Katsina da sauran wuraren da ke fama da matsalar, har sai an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kafin wannan ziyara,sai da muƙaddashin gwamnan yayi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu cikin gaggawa ya kawo wa jihar ɗauki dangane da ƙaruwar hare haren yan bindiga a wasu sassan jihar.

Tuni dai tawagar gwamnatin jihar ƙarƙashin sakataren gwamnati Barista Abdullahi Garba Faskari da kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro da manyan jami’an tsaro sukai kai ziyarar ta’aziyar rasuwar waɗannan mutane a unguwar Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi.

By ukarofi