Daga USMAN KAROFI
A ranar Asabar, sojojin Isra’ila sun kai hare-hare kan wasu sansanonin sojin Iran da ke yankuna kamar Ilam, Khuzestan, da Tehran, inda aka auna wurare kusan 20 a cikin sa’o’i kadan. Iran ta tabbatar da mutuwar sojojinta biyu, tare da bayyana cewa harin ya haifar da ƙaramin ɓarna kawai. Wannan harin ya zama wani babban ci mataki a tsakanin rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Kakakin sojin Isra’ila, Daniel Hagari, ya ce Isra’ila ta kammala wannan aikin nata kuma ta shirya kare kanta idan Iran ta mayar da martani. A nasa ɓangaren, Hedikwatar Tsaron Sama ta Iran ta ce hare-haren sun ci tura sakamakon martanin tsaron kasar. Haka kuma, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa tana da haƙƙin kare kanta daga duk wani hari daga waje.
Martanin Kasashen Duniya
Amurka
Kakakin Kwamitin Tsaron Ƙasa na Amurka, Sean Savett, ya yi kira ga Iran ta dakatar da hare-harenta kan Isra’ila, yana mai cewa hakan zai ba wa ɓangarorin damar cimma zaman lafiya maimakon ƙara rura wutar rikici. Ya bayyana cewa Amurka ba ta da hannu a cikin wannan hari, amma tana goyon bayan ƙoƙarin diplomasiyya don rage tashin hankali a yankin. Pentagon ya tabbatar da cewa Amurka na goyon bayan Isra’ila don kare kanta.
Qatar
Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ta yi Allah wadai da hare-haren, tana mai cewa Isra’ila ta keta ikon Iran tare da yin kira ga dukkan ɓangarorin su nuna hakuri su maida hankali kan magance rikicin ta hanyar tattaunawa. Qatar ta kuma nemi duniya ta ɗauki matakan da za su kawo ƙarshen rikicin Gaza da Lebanon don rage damuwar yankin.
Masar
Masar ta yi Allah wadai da duk wani abu da zai iya kawo barazana ga tsaro da kwanciyar hankali a yankin. Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta yi kira da dakatar da rikicin da ke cikin Gaza tare da shirin sako dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su a matsayin hanyar kawo zaman lafiya.
Saudiyya
Saudiyya ta bayyana harin da Isra’ila ta kai wa Iran a matsayin take ikon ƙasar ta da saɓa wa dokokin Ƙasa da ƙasa, tana mai kira ga ɓangarorin su yi hakuri su guji ɗaukar matakan da za su kara tsananta rikicin da zai kawo barazana ga tsaron yankin.
Turkiyya
Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana cewa Isra’ila tana yin ayyukan da suka kai ga kashe-kashe da lalacewa a yankin, tana mai cewa hare-haren suna jawo barazana ga tsaron ƙasa da ƙasa. Turkiyya ta yi kira ga ƙasashe duniya su ɗauki matakan dakatar da harin Isra’ila domin kare zaman lafiya a yankin.
Kasashen Larabawa da Dama
Kasashe irin su Jordan, Kuwait, da Iraq duk sun bayyana damuwarsu game da hare-haren Isra’ila, suna mai kira ga ɗaukacin ɓangarorin su ja da baya daga duk wani abu da zai ƙara haddasa tashin hankali. Kuwait ta bayyana Isra’ila da bin wata manufa ta tada hankalin yankin da kuma barazanar tsaro.
Ƙungiyar Hamas
Hamas ta soki hare-haren, tana mai cewa hakan wani yunkuri ne da ke ƙara kawo haɗarin tsaro a yankin da kuma jefa rayukan al’umma cikin hatsari. Ta kuma ce Isra’ila ce ke da alhakin abinda ka iya faruwa sakamakon hare-haren.
Majalisar Ɗinkin Duniya da Kasashen Yammacin Turai
Manyan ƙasashe da ƙungiyoyin duniya sun bayyana buƙatar dakatar da duk wasu matakan da ke ƙara tayar da hankali a yankin, suna mai cewa akwai buƙatar ɗaukar matakan kawo zaman lafiya don rage rikicin da ke gabatowa.
Ƙasashen duniya sun mayar da martani mai karfi game da hare-haren, suna mai kira ga Isra’ila da Iran su guji duk wani mataki da zai ƙara dagula al’amura a yankin.