Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a lokacin da yake buɗe taron Arewa maso Yamma kan gyara ga tsarin mulkin jam’iyar ta APC.
Taron da ya gudana a gidan gwamnatin Jihar Katsina ya sami halartar mataimakin gwamnan Sokoto da kakakin majalisar dokoki na jihohin Kebbi, Jigawa da Sokoto da wakilan sauran jihohin Arewa maso Yamma.
Dikko Raɗɗa ya danganta bunƙasa da jam’iyar APC ke yi da irin salon shugabanci na shugaban ƙasa Bola Tinubu.
“Ina kan gaba wajen kafa jam’iyar APC don haka a yau ina mai farin cikin ɗaukan baƙuntar wannan kwamiti a jihar ta,” Inji Dikko Raɗɗa.
Gwamnan yayi kira ga ya’yan jam’iyar da ko da yaushe su zama masu biyayya ga shugabancin jam’iya “biyayya ga shugabancin jami’iya ya kawo mu matsayin da muke yanzu,”Inji malam Dikko Raɗɗa.
Ya yaba da salon shugabancin Bola Tinubu da yace shine dalilin da yasa a kullum jam’iyar APC ta ke ƙara tagomashi.
Dikko Raɗɗa ya bayyana a Jihar Katsina babu wata jam’iyar adawa domin a cewar sa duka zaɓaɓɓun wakilai a matsayin jiha da ƙasa duka daga jam’iyar APC suka fito.
“Sanatoci guda uku, Yan majalisar tarayya guda 15,yan majalisar dokokin jihar guda 34, shugabannin ƙananan hukumomi 34 duka ya’yan jam’iyar APC,”inji Gwamnan jihar.
Ya ƙara da cewa haka zai sake faruwa a zaɓen 2027 a jihar,ya kuma tabbatar da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu shi zai sake lashe zaɓe mai zuwa.
Gwamna ya bayyana ƙoƙarin da a ke yi na gyaran tsarin mulkin jam’iyar da yace abu ne mai muhimmanci kuma ya zo akan lokaci.
“Yakamata a lokaci lokaci ana gyara tsarin mulkin jam’iyar domin ya tafi dai dai da zamani,”inji Dikko Raɗɗa.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da shugabannin jam’iyar APC na jihohin Arewa maso Yamma da masu ruwa da tsaki na jam’iyar a Katsina.
