ASIKO ya ƙaddamar da shirin sauya wa ababen hawa amfani da fetur zuwa iskar gas

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

A daidai wannan lokaci da tsadar man fetur ke ta’azzara tsadar harkokin sufuri wani kamfanin iskar gas mai suna ASIKO Holding Energy ya vullo da tsarin sauyawa ababen hawa masu aiki da fetur zuwa na gas.

Da yake zantawa da ‘yan jarida, Manajan kasuwanci da hulɗa da jama’a na kamfanin Kwamared Haruna Wakili ya ce tun sama da shekaru 15 suke harkar gas a ƙara nan sun zo da wannan tsari ne saboda zamani ya zo ana taƙaita amfani da man fetur saboda yana gurɓata muhalli, shi ya sa ake cire masa tallafi da ya yi tsada sai a koma wasu abubuwa da ya fi sauƙi.

Ya ce yanzu a duniya ana sauyawa da ga amfani da fetur zuwa gas shi ya sa gwamnatin tarayya ta fito tsari yadda za ta inganta amfani da gas wajen harkar sufuri a ƙarƙashin shugabancin Dakta Muhammad Ibrahim shugaban National Gas Expansion Programme a ƙarƙashin kulawarsa aka amince a faɗaɗa fasaha da za a riƙa juyar da motoci da sauran ababen hawa dake amfani da fetur su dawo amfani da iskar gas.

Ya ƙara da cewa kamfaninsu na ASIKO na da ga na farko a Arewa da ya ƙaddamar da fasahar a Kano ranar 25 ga oktoba 2023 aka soma da mayar da baburan Adaidai sahu da motocin bas na ‘yan ƙurƙura masu aiki da iskar gas hakan zai sama musu sauƙi na kaso 50 cikin 100.

Ya ce nan gaba kaɗan za su samar da cibiyoyin da za a riƙa ɗuwawa ababen hawa gas sannan tukunyar gas da ake amfani da shi yana da inganci da kariya daga kamawa da wuta wacce an samo fasahar ne daga ƙasar Ingila da Turkiyya.

Ya ce akwai matakai na kariya da za a riƙa yi wa mutane bita akai don ya kasance kowa ya karɓa. Ita ma Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da motoci da za su riqa amfani da iskar gas kuma suna sa ran za su samu tallafi daga Gwamnatin Tarayya da za a sauƙaƙawa al’umma kuma shirin ya yi saurin yaɗuwa.

Yanzu haka suna haɗa bayanai don su gane waɗanda aka juyarwa ababen hawansu da ga tsarin man fetur zuwa iskar gas adadin awanni yake ɗauka dan komai ya fito a zahirance idan ansa fetur lita kaza adadin tafiyar kilomita nawa yake idan kuma aka sa gas nawa yake dan gane wannene ya fi sauƙi.

Kwamared Haruna Wakili ya ce haka ma sun juyar da injunan wutarsu zuwa na iskar gas irin amfaninda suke gani kan hakan ba za su iya yin komawa amfani da fetur ba.

Ya ce suna kyakkyawan dangantaka da hukumomi da ke kula da haɗurra daka iya aukuwa sannan wannan abune da yanzu ma ake son yin dokokinsa sai ma an vullo da wasu hukumomin, domin a baya ana kula da abinda ya shafi gidaje ne da ke amfani da iskar gas, amma yanzu ya zama har da na wanda za a sawa ababen hawa na sufuri domin masu adaidaita sahu kawai a jihar Kano sun kusa miliyan in yan KAROTA kaɗai ne za su kula da ababen hawa, waɗanda za su yi amfani da gas aikin zai musu yawa sai an samar da wasu hukumomin dan abin ya yi sauƙi dan kare rayuka da dukiyoyi.

Wakili ya ce koyaushe a shirye suke su da suke harkar gas idan Gwamnati ta nemi shawarwarinsu za su bata yanda abubuwa za su tafi da sauqi su sana’arsu bata tavu ba itama gwamnati abinda doka ta ɗora mata na kula da al’umma da tsare rayuka da dukiyarsu bai taɓu ba tallaliin arzikin bai taɓu ba sai dai ya ƙaru.

Alhaji Haruna Wakili ya ce yanzu haka jama’a suna ta nuna sha’awarsu akan abin saboda ganin kwarewa da inganci da kariya da aka baiwa tsarin kuma tsarin nada sauƙi da riba ga masu ababen hawa da zai sauƙaƙa.

By Editor