Faransa za ta maido wa Nijeriya $150m wadda Abacha ya wawushe

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana a ranar Juma’ar da ta gabata cewa, ƙasar Faransa za ta maido wa Nijeriya kuɗi har Dala miliyan 150 wanda tsohon Shgugaban Ƙasa marigayi Janar Sani Abacha ya wawushe a halin rayuwarsa.

Cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Faransa da matakin maido da kuɗin da ta ɗauka.

Da yake karɓar baƙuncin Ministar Harkokin Wajen Faransa, Catherine Colonna, Shugaba Tinubu ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Faransa, yana mai cewa, fahimtar juna da ke tsakanin ƙasashen biyu ya sa ya ziyarci Paris bayan da aka rantsar da shi.

“Na gode da wannan labari mai daɗi game da maido da kuɗaɗen da Abacha ya sace. Muna godiya da haɗin kanku wajen maido da kuɗaɗen Nijeriya. Za a yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace wajen gina ƙasarmu,” kamar yadda aka rawaito Tinubu ya faɗa.

Yayin da yake jaddada buƙatar ƙarfafa haɗin kai a tsakanin ƙasashen biyu, musamman a ɓangaren sha’anin siyasa da tattalin arziki, Tinubu ya kuma yi na’am da ra’ayi guda da ƙasashen biyu ke da shi kan abin da ya shafi ɗumamar yanayi, ɓangaren ilimi, raya al’adu da sauransu.

Kazalika, Tinubu ya ce ƙasashen biyu sun rattaɓa hannu kan yarjejeniya ta €100 miliyan domin tallafa wa shirin i-DICE, shirin da Nijeriya ta ƙirƙiro don bunƙasa sha’anin zuba jari da fasahar sadarwa (ICT) da kuma masana’antar ƙirƙire-ƙirƙire.

By Editor