Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Kimanin naira miliyan biyar Ƙungiyar Izala ta ravawa mata 500 da ke riqe da marayu a Gombe inda kowacce ta samu naira dubu goma a matsayin tallafi.
Ƙungiyar Izala ta raba tallafin ne a ƙarƙashin Kwamitin Nisa’us Sunnah da ta kafa a Gombe ta zaƙulo mata iyayen marayun suka ci gajiyar shirin.
Da yake jawabi a wajen taron Babban Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, jan hankalin iyaye mata ya yi da cewa su maida hankali wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yan da aka mutu aka bar su da su domin Allah zai tambaye su.
Kabir Gombe, ya ce waɗannan yara haƙƙi ne Allah ya ɗora musu kuma zai tambaye su yadda suka kula da su.
Sannan ya ce kula da maraya akwai falala sai ya bada gudunmawar naira dubu 100 na asusun ginin makarantar marayu da ake yi.
Shi ma Shugaban Ƙungiyar JIBWIS na Jihar Gombe Injiniya Salisu Muhammad Gombe, bayyana wannan aiki na kwamitin Nisa’ussunnah ya yi a matsayin gagarumin aiki wanda irin sa ne ake buƙata a wanann yanayi da ake ciki domin tallafawa marayu da waɗanda suke riƙe da marayun.
Injiniya Salisu Gombe, ya ja hankalin al’umma musamman masu hannu da shuni da muƙarraban gwamnati da su shigo lamarin domin bada ta su gudumawar.
Daga nan sai ya ce hatta gwamnati yana da kyau ta shigo wajen haɗa kai da ƙungiyar Izala don haɗa ƙarfi da qarfe wajen aiwatar da irin wadannan ayyuka.
Da take tsokaci a wajen Babbar Jojin Jihar Hajiya Halima S. Muhammad, kira ta yi ga iyaye mata da cewa su kasance masu kula da marayun domin suma Allah zai kula da na su bayan basa nan, sannann kuma su jajirce wajen bai wa ‘ya’yan nasu tarbiyya.
Haka zalika shi ma Shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Gombe Alhaji Usman Ali Ashaka, kiran al’umma ya yi da su kula da yaransu su kuma miqa rahoton duk wani ɓatagari da ke cikin al’umma da ba su yarda da take-taken su ba domin ɗaukar mataki.
Taron ya samu halartar manyan mutane masu sarautun gargajiya da shugabannin addini malamai da sauran al’umma.
