Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A taron da ta gudanar karo na 118 hukumar zartarwa na ƙungiyar makarantun kimiyya da fasaha ta jihar ta bai wa gwamnatin Katsina wa’adin kwanaki 15 da ta biya wasu alawaus nasu bisa yarjejeniya da ƙungiyar ta cimma da gwamnatin tarayya.
Wannan alawus sune ake cewa Consolidated Academic Tools Allowance (CATA) da Earned Academic Allowance (EAA) da ya fara daga watan Janairun 2026.
Bayan zartar da wannan yarjejeniya ga ma’aikatan makarantun na gwamnatin tarayya, ƙungiyar ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta tura wa gwamnatocin jihohin ƙasa baki ɗaya ta na sanar dasu wannan alkhairi da ya samu, kuma da buƙatar a aiwatar da shi ga takwarorin su dake makarantun jihohin ƙasar nan.
A cikin zantawa da shugaban ƙungiyar reshen kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina da ke Katsina watau Kwamared Muhammad Nasir Gidado, ya bayyana wa manema labarai cewa, wannan sakon gargaɗi ya kai gidan gwamnatin jihar Katsina, kuma wa’adin ya fara ne tun ranar Talata 27 ga watan Oktoba, 2026.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar na da rassa a manyan makarantun jihar kamar haka:
Hassan Usman Katsina Polytechnic, Katsina da Katsina State Institute of Technology and Management sai
College of Health Sciences, Katsina
da kuma College of Nursing Sciences Katsina.
Ya yi kira ga gwamnan jihar Katsina da ya duba wannan al’amari ya zartar dashi cikin lokaci kamar yadda ya yi wa wasu a cikin jihar.
Basu sanar da matakan da za su ɗauka ba bayan da wa’adin da suka bada ya ƙare.
