ASUU ta samu biliyan N52.5 daga hannun Gwamnatin Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta biya malaman jami’o’i Naira biliyan 30 na asusun farfaɗo da ilimi da kuma alawus-alawus na ilimi da suka samu Naira biliyan 22.5, tare da jaddada cewa ta samu cigaba sosai wajen aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma da ma’aikatan jami’o’in.

Ministan Ƙwadago, Sanata Chris Ngige shi ne ya tabbatar da hakan yayin tattaunawarsu da jaridar THISDAY a wannan ƙarshen makon a lokacin da yake ƙarin haske kan halin da ake ciki tsakanin gwamnati da ƙungiyar ASUU.

Ministan ya ce ya samu sanarwa daga Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya kan cewa an sakar wa jami’o’i kuɗaɗe don farfaɗo da jami’o’in da kuma alawus-alawus na ilimi ga ma’aikata.

Ya ce a Juma’ar da ta gabata Babban Akanta da kuma Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya “sun faɗa mini cewa sun biya kuɗaɗen alawus ga jami’o’in tarayya guda 38 kuma ya zuwa Asabar kowace jami’a ta samu kuɗinta don biyan ma’aikatanta.”

Yana mai cewa, “Na sanar da shugabannin ASUU matsayar gwamnati.”

Haka nan, Ngige ya ce an kammala da batun tsarin biyan albashin jami’o’i na UTAS har ma Hukumar Bunƙasa Fasahar Bayanai (NITDA) ta miƙa rahotonta ga gwamnati.

Kafin wannan lokaci, ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki muddin Gwamnatin Tarayya ta gagara biya mata buƙatunta kamar yadda ta ce sun cimma yarjejeniya a can baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *