EFCC na bincikar wani gwamnan Arewa kan fitar da Naira Biliyan 60 a banki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa tu’annati (EFCC), ta tuhumi wani Gwamnan Arewa bisa zargin fitar da kuɗi har Naira biliyan 60 daga baitulmalin jihar da kansa.

Hukumar EFCC, wacce ta bayyana hakan a yau a cikin sabuwar sanarwarta, ta ce, gwamnan ya fito ne daga yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar nan amma ba ta bayyana sunansa ba.

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, wanda ya yi magana a sanarwar, ya ce, “zan iya gaya muku cewa sabuwar sashen leƙen asirin da muka ƙirƙiro ne yake yin irin waɗannan abubuwan al’ajabi.”

Ya ce, “sashen ya bankaɗo abubuwa sosai. A ɗaya daga cikinsu, wani gwamna a jihar Arewa ta tsakiya a cikin shekaru shida da suka gabata (mutum ɗaya) ya cire maƙudan kuɗi har sama da Naira biliyan 60.”

“Duk waɗannan muna duban su, kuma ina tabbatar muku da cewa a ƙarshen dukkan binciken da muke yi, za mu bayyana wa ‘yan Nijeriya abubuwan da muke yi a bayan fage na aikata laifuka ta yanar gizo, da waɗanda aka fallasa a siyasance da kuma cuɗanya da hukumomin gwamnati wajen tabbatar da cewa muna da ingantattun matakai da tsare-tsare kan yadda ake gudanar da harkokin gwamnati,” inji Bawa.