Korona: Hana ‘yan Nijeriya zarya zuwa wasu ƙasashe ya fusata Buhari, ya ce sai ya rama

Daga BASHIR ISAH

A matsayin wani mataki na maida martani kan hana ‘yan Nijeriya shiga wasu ƙasashen duniya saboda korona, Gwamnatin Tarayya ta ce daga ranar Talata mai zuwa, 14 ga Disamba, za ta haramta wa jiragen saman da suka fito daga Canada da Birtaniya da kuma Saudiyya shigowa Nijeriya.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, shi ne ya bada sanarwar ɗaukar wannan mataki a Legas ranar Lahadi, inda ya ce an ɗauki matakin ne don maida martani kan ƙasashen da suka haramta wa jiragen da suka fito daga Nijeriya shiga cikinsu domin ɓarkewar sabon nau’in cutar korona mai suna ‘Omicron’.

Kazalika, Sirika ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta sanya ƙashen Birtaniya da Canada da Saudi Arebiya daga jerin ƙasashen da ta ɗaga wa jan kati sakamakon ɓarkewa da kuma yaɗuwar koronar ‘Omicron’.

Ministan ya ƙara da cewa Nijeriya za ta gani ko waɗannan ƙasashen da suka hana Nijeriya shiga cikinsu suna da ‘yancin da jiragensu za su shigo Nijeriya ta fuskar kasuwanci.

A cewar Sirika, “Akwai batun sanya Nijeriya daga jerin ƙasashen da ta haramta wa shiganta da Saudiyya ta yi. Na samu halartar wani taro a ranar Lahadi tare da kwamitin yaƙi da korona.

“Inda muka bayyana ra’ayinmu cewa ba mu yarda da hakan ba, tare da bada shawarar a saka Canada da UK da Saudi Arabia da kuma Argentina a cikin jerin kasashen da aka ɗaga wa jan kati.

“Kamar yadda suka yi mana, idan suka hana ‘yan ƙasarmu shiga ƙasashensu, mu ma ba za mu bari jiragensu su shigo ƙasarmu ba.

“Sam bai kamata su shigo ba. Na tabbata nan da kwana uku, Litinin ko Talata, za mu shigar da dukkanin wadannan ƙasashe cikin jerin ƙasashen da aka ɗaga wa jan kati saboda korona.”

Sirika ya jaddada cewa an haramta wa jiragen ƙasashen da lamarin ya shafa shigowa Nijeriya.

A ƙarshe, Sirika ya bai wa ‘yan Nijeriya masu niyyar tafiya waɗannan ƙasashe da lamarin ya shafa haƙuri, tare da cewa matakin da Gwamnatin Nijeriya ta ɗauka don amfanin ‘yan ƙasa ne.