An zaɓi Samuel Eto’o ya zama shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na Kamaru

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An zaɓi shahararren ɗan ƙwallon Kamaru, Samuel Eto’o a matsayin shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (FECAFOOT) a ranar Asabar, wata ɗaya kafin ƙasar ta karɓi baƙuncin gasar cin kofin Afrika.

Tsohon ɗan wasan gaba Eto’o, wanda ya taka leda a Barcelona, Inter Milan da Chelsea, zai karɓi ragamar ƙungiyar da ta daɗe tana fama da rigingimu, rashin gudanar da mulki da kuma zargin cin hanci da rashawa.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta shiga tsakani sau da yawa don kawo ƙarshen cece-kuce tsakanin jami’an FECAFOOT.

Eto’o mai shekaru 40 ya lashe zaɓen da ƙuri’u 43 daga mambobin babban taron FECAFOOT. Abokin hamayyarsa, shugaban mai ci Seydou Mbombouo Njoya, ya samu ƙuri’u 31.

Kamaru za ta karɓi baƙuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka daga ranar 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabrairu, an kuma kwace mata damar karɓar baƙuncin gasar a shekarar 2019 saboda jinkirin shirye-shirye da kuma matsalolin tsaro.