Dole ne a ɗore da yaƙi da cin hanci da rashawa

Ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne al’ummar duniya suka ware a matsayin ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta duniya. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙuduri mai lamba 58/4 na ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2003 ta ware ranar 9 ga watan Disamba na kowace shekara a matsayin ranar wayar da kan jama’a game da laifukan da ke kawo cikas ga ci gaba da kuma talauta jama’a.

Har ila yau, rana ce ga shugabannin siyasa, gwamnatoci, hukumomin shari’a, ƙungiyoyin fafutuka da qungiyoyin farar hula don sabunta alqawurran da suka ɗauka na kawar da wannan abu da aka gano a matsayin wani lamari mai sarƙaƙiya na zamantakewa da siyasa da tattalin arziki wanda ya shafi dukkan ƙasashe.

Taken bikin na bana shi ne ‘Haƙƙinku, Matsayinku: Ku Ce A’a ga Cin Hanci da Rashawa.’ Tana neman ganin waɗanda laifin ya shafa su mai da hankali kan wannan barazana a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga ci gaban zamantakewa da ci gaban tattalin arziki a duk inda aka samu gindin zama.

Kimanin shekaru 15 bayan ƙaddamar da taron wayar da kan jama’a na shekara-shekara, sabuwar ƙididdigar cin hanci da rashawa ta nuna har yanzu yawancin ƙasashen duniya ba su samu ci gaba ko kaɗan a yaƙin da ake yi da cin hanci da tashawa a duniya.

Haƙiƙa, an san cin hanci da rashawa a matsayin cuta mai saurin yaɗuwa da ke addabar ƙasashen duniya daban-daban. Yana iya ruguza kowace al’umma, ya hana ci gabanta, da gurgunta mulkin dimokuraɗiyya, ya haifar da gwamnatoci marasa inganci, da kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa da kawo cikas ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki. Wannan dodo yana bayyana ta hanyoyi daban-daban kamar, cin hanci da rashawa, rashin aiki da ilimi da wawure dukiyar jama’a.

Babu wata ƙasa guda da ke samun tsaftataccen lissafi na lamarin kamar ƙasashen da aka ware a matsayin masu tasowa da marasa ci gaba sun duk fi fama da matsalar. Nijeriya ta yi fama da matsalar cin hanci da rashawa a cikin shekaru ɗaya da rabi da suka wuce. Ta kasance ta 143 a shekara ta 2011, ta 139 a shekarar 2012 da ta 144 a shekarar 2013. Kamar yadda yake a shekaru huɗu da suka gabata, tana matsayi na 136 daga cikin ƙasashe 175, a cewar ƙididdigar cin hanci da rashawa ta ‘Transparency International’ (TI).

Denmark har yanzu tana riƙe da matsayi na farko a matsayin qasa mafi ƙarancin cin hanci da rashawa a duniya daga cikin ƙasashe 175 da TI ta bincika. Botswana ita ma ta riƙe matsayinta na farko a matsayin ƙasa mafi ƙarancin cin hanci da rashawa a Afirka kuma ta 31 a duniya. A kimantawar shekarar 2017 da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta yi, Nijeriya ce ƙasa ta 148 a cikin ƙasashe 175 mafi ƙarancin cin hanci da rashawa.

Da dama daga cikin masu sa ido kan cin hanci da rashawa a ciki da wajen ƙasar nan sun danganta nasarar da Nijeriya ta samu a yaƙin da ake yi da dodanniya da sabon ƙarfin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa yaƙin tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2015. Amma yaƙin bai yi nisa ba duk da cewa an samu nasara a samuwar wasu gavovin yaƙi da rashawa da kuma matakan da aka sanya don yaƙarsa.

A baya-bayan nan dai cin hanci da rashawa ya ƙaurace wa ƙatutu saboda waɗanda ke riƙe da madafun iko sun nuna rashin kishin ƙasa wajen bai wa hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata musamman a gwamnatin da ta shuɗe.

Lamarin da ya zama dole hukumomi su karɓi takardar ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kafin a gurfanar da wasu masu cin hanci da rashawa a gaban kuliya domin shari’a, ya sa abin ke ta tafiyar katantanwa.

Duk gwamnatin ta himmatu wajen ganin ta kawar da cin hanci da rashawa a rayuwarmu ta ƙasa, dole ne ta baiwa hukumomin damar aiwatar da aikinsu na yaƙin.

Wani abin lura kuma shi ne wani manufar da Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da shi. Dabarar ta haifar da sakamako mai kyau kafin a daga baya kuma a yishuru da batun.

Ƙasashe da dama a faɗin duniya sun ɗauki tsauraran matakai don daƙile barazanar. Misali Chana ta zartar da hukuncin kisa ga waɗanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa. Wani abin mamaki shi ne wasu manyan ‘yan Nijeriya sun ba da shawarar a yi wa Nijeriya irin wannan doka.

Ya kamata gwamnatin Buhari ta ci gaba da yin amfani da ra’ayin mafi yawan ’yan Nijeriya tare da ci gaba da yaƙi da cin hanci da rashawa ba tare da la’akari da sanwar sa ba har sai an durƙusar da dodon, hakan zai samu ta hanyar ƙarfafa hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawada kuma hanzarta shari’ar cin hanci da rashawa da ke addabar kotunan mu da kuma ƙara ƙaimi wajen ƙwato kadara. Cin hanci da rashawa sun fi ‘yan bindiga muni. Kamar yadda marigayi tsohon shugaban Ghana Jerry Rawlings ya taɓa furtawa, “’Yan bindiga suna satar mutane amma masu cin hanci da rashawa suna satar al’umma ne.”

Mummunan laifukan da ke talauta talakawa da kuma kawo cikas ga ci gaba dole ne a magance shi tare da duk abin da ya cancanta. Hukuncin da wasu manyan ma’aikatan gwamnati, da masu riqe da muƙaman siyasa suka yi ya zama kyakkyawan ci gaba.

Ya kamata hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su ci gaba da gudanar da ayyukansu. Yaƙi da cin hanci da rashawa wani aiki ne da ya kamata mu goyi baya idan har ana son ci gaban aasa, in ba haka za mu rasa makomarmu gabaɗaya.